Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kalandar shekarar 2020 a cikin hotuna: Waiwaye kan shekarar da ta zama ta daban
Kun tuna lokacin da ɗaukacin mutanen duniya a ƙarshen 2019 suke cike da fata da burin shiga sabuwar shekara?
To abubuwa da ba su tafi yadda aka yi zato ba. Annobar cutar korona ta mamaye duniya, abin da ya jawo matuƙar damuwa a zuƙatan mutane.
Amma shekarar 2020 ta wani wajen ta zama kyakkyawa, mai ban dariya da jajircewar ɗan adam, kamar yadda waɗannan hotunan daga kowanne wata cikin watanni 12 na shekarar ke nunawa.
JANAIRU
Wata mummunar cuta ta bayyana daga China kuma ba a san abubuwa da yawa a game da ita ba. A lokacin da babu wani abu sahihi na kariya, sai wasu mutanen suka dinga amfani da wasu kayayyakin amfanin yau da kullum a matsayin kariya.
FABRAIRU
Fitowar wata ɓaro-ɓaro a ganshi da girmansa da haskensa da ba safai irin haka yake faruwa ta bai wa mutane mamaki a faɗin duniya.
An ɗauki hoton ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a sararin samaniya da aka gani a wannan shekarar a garin Edirne na Turkiyya, a kusa da hasumayoyin Masalacin Selimiye da aka gina tun ƙarni na 16.
MARIS
Da yawan mutane sun shafe mafi yawan lokacinsu a shekarar 2020 a intanet suna mu'amala da abokai ko yin aiki ko sayayya sakamakon matakan da aka sanya na annobar cutar korona - kamar dai yadda wannan malamin a Hong Kong yake naɗar darasin da zai yi wa ɗalibansa ta intanet.
AFRILU
Matakan bin dokar yin nesa-nesa da juna sun bayyana basirorin mutane da dama. Wani malamin addinin kirista na ɗariƙar Roman Katolika a Amurka ya bi matakin ba da tazarar ta hanyar amfani da bindigar roba da ke fesa ruwa don sanya albarka ga masu ibada da ruwa mai tsarki.
MAYU
Kisan da aka yi wa wani Ba-amurke ɗan asalin Afirka George Floyd a hannun ƴan sanda ya janyo an ƙaddamar da zanga-zanga a faɗin duniuya kan adawa da wariyar launin fata da cin zarafin da ƴan sanda ke yi.
Wannan zanga-zangar da aka yi a Sacramento da ke California, ita ce ta farko daga cikin wadanda suka biyo baya a faɗin ƙasar.
YUNI
A lokacin da ake sa ran za a ɗage dokar kulle ta farko, an gabatar da kaɗe-kaɗe ga tsirrai fiye da 2,000 a wani gidan raye-wata a Barcelona. Hakan wani ƙoƙari ne na nuna muhimmancin kiɗa a lokacin da ake cikin yanayi maras daɗi.
YULI
Wata ƴar Kenya tana tsaye cikin halin gazawa tana kallon yadda farin ɗango ke sauka a kan gonarta.
Bayan da ƙwarin suka lalata gonaki a faɗin Iran da Pakistan da Indiya, sai kuma suka bazu a Gabashin Afirka.
AGUSTA
Daya daga cikin fashewa mafi muni a tarihi ta auku a cibiyar makamashin mukiliya a tashar jiragen ruwa ta Beirut a Lebanon. Fiye da mutum 200 sun mutu yayin da dubbai suka ji raunuka.
A wannan hoton wani mai buga fiyano Raymond Essayan ne wanda ya gamu da rikicewar ƙwaƙwalwa sannan ya rasa muhallinsa.
SATUMBA
Dajin Amazon na Brazil ya gamu da bala'in gobarar daji mafi muni a cikin shekara 10 da suka gabata, abin da ya ɗaga hankalin masu kula da muhalli da ƙungiyoyin killace muhalli.
Wannan damisar ta tsira daga wutar a Pantanal, amma ta ƙone a yatsunta.
OKTOBA
Gwamnatoci a faɗin duniya suna ta faɗi tashi kan ko dai su sassauta ko su ƙara tsananta dokokin kulle a yayin da ake samun ƙarin masu kamuwa da kuma masu warkewa daga cutar korona.
Kamfanoni da masana'antu da dama sun ce suna fargabar abin da zai je ya komo a gaba saboda cutar korona. Wannan kantin cin abincin da ke Rome babban birnin Italiya sun ajiye ƙwarangwal don su nuna yadda kasuwancinsu ke mutuwa.
NUWAMBA
Mitree Chitinunda daga Thailand ya kasance mai goyon bayan gidan sarauta sosai. Amma jerin zanga-zangar da aka yi ta yi a bana da ba a taɓa yin irinsu ba don neman kawo sauye-sauyen dimokraɗiyya da karya lagon tsarin masarauta sun sa ya sauya aƙidarsa.
A yanzu gashin kan Mitree na nuna alamun yatsu uku da ya samo asali daga tsarin Hunger Games da kuma yadda masu zanga-zanga suke amfani da shi a faɗnin Thailand.
DISAMBA
Cutar korona na ci gaba da yaɗuwa a duniya, amma ba a fasa komai a gasar zuwa duniyar wata ba.
Kumbon da China ta tura duniyar wata a shirinta na Chang'e-5 ya yi nasarar zuwa da dawowa duniya bayan ya kwaso samfurin ƙasar duniyar wata da aka taɓa samu a cikin shekara 44.
Dukkan hotunan suna da haƙƙin mallaka.