'Daga waje' aka kai hari kan tankar man fetur a Saudiyya

An wallafa

Wasu daga wajen Saudiyya sun kai hari kan wani jirgin ruwan tankar man fetur mai dauke da tutar Singapore, lamarin da ya kai ga tashin gobara da babbar fashewa ranar Litinin.

Jirgin ruwan mai suna the BW Rhine, yana sauke man da ya dauko a tashar jiragen ruwan Jeddah da ke Saudiyya lokacin da lamarin ya faru.

"Harin ya sa an samu babbar fashewa da kuma tashin gobara," a cewar kamfanin da ya mallaki jirgin Hafnia a wata sanarwa.

Kamfanin ya kara da cewa ma'aikatan jirgin ruwan sun kashe wutar kuma babu wanda ya jikkata, ko da yake wasu bangarorin jirgin sun lalace.

"Mai yiwuwa man da ke cikin jirgin ruwan ya kwaranye, amma ba a tabbatar da hakan ba kuma binciken da aka yi ya nuna cewa adadin man da ke cikin tankar daidai yake da wanda aka dauko tun da farko kafin a kai harin," a cewar Hafnia.

Jirgin ruwan na The BW Rhine yana iya daukar tan 60,000 zuwa 80,000 na man fetur, a cewar Hafnia. Yana dauke da kashi 84 na man da ake zuba masa lokacin da lamarin ya faru, in ji masu kamfanin.

Tashar jiragen ruwan ta Jeddah, ita ce babbar tasha a Bahar Maliya kuma cibiyar da babban kamfanin man fetur na Saudiyya Saudi Aramco yake raba mai daga cikinta.

'Yan tawaye ne 'suka kai hari'

Harin na faruwa ne bayan wata fashewar tankar mai ta kasar Girka, wadda ta isa tashar jiragen ruwan Shuqaiq da ke Saudiyya, harin da dakarun sojin Saudiyya suka dora alhakinsa kan 'yan tawayen Houthi da ke Yemen.

Aramco ya ce harin ya yi wani babban rami a jikin tankar man, lamarin da ya haddasa babbar fashewa da tashin gobara.

Wannan harin ya nuna irin barazanar da rijiyoyin man fetur na Saudiyya ke fuskanta.