Kayatattun hotunan Afrika na wannan makon daga ranar 4 zuwa 10 ga watan Disamba 2020

An wallafa

Zaɓabbun hotunan nahiyar Afrika na wannan makon.

Wata yarinya sanye da kaya shuɗaye cikin wani murmushi mai haɗe da kunya ta riƙe kifin roba.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata yarinya ɗuke da kifin roba a yankin Kyebi da ke kudancin Ghana a ranar Litinin.
Wani mutum a gefen titi yana zana hoton wata mata a jikin tutar Liberia.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mai zane Saah John a ranar juma'a yana zane a Monrovia babban birnin Liberia.
Wani mutum yana tafiya cikin gaggawa ta gefen wani sabin zanen filawa a kan titi

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A Afrika ta Kudu, wannan ƙaton zanen da ake gani shi ne na baya-bayan nan da aka zana a kan titin Johannesburg.
Masu atisayen gina jiki sun tasu suna motsa jininsu a bayan fage, wasu kuma na tattaunawa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, 'Yan takara na kintsa kansu a bayan fage a wata gasar daga ƙarfe ta masu gina jiki a ranar Asabar
Maza masu gina jiki na rawa a kan dandali a jere a layi.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kimanin mutum 130 daga gabashin Afrika ne suka shiga gasar da ta gudana Nairobi babban birnin ƙasar Kenya.
Wani mutum a sama ya yi tsalle zai faɗa ruwa. A bayansa kuma akwai taron yara da ke jiransa ya faɗa su biyo shi, wasu kuma tuni sun cikin ruwan.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani taron maza manya da yara na wasan ninƙaya a kogin Hamdayit na Sudan, wanda ya yi iyaka da ƙasar Habasha.
Wasu jijiyoyin ruwa jefi-jefi da ake gani a saman teku.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A gobe ne a ke sa ran wani jirgin ruwa a Cape Town da ke Afrika ta Kudu, zai yi wani zagaye a irinsa na farko a kogin Atlanta.
Wasu masu kamun kifi su biyu dauke da kifi a bokiti a kawunansu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Alhamis wasu masu kamun kifi a bakin ruwan Paquitequete da ke Mozambique. Kimanin mutum dubu ɗari biyar aka tilastawa barin gidajensu a yankin Cabo Delgado a wani rikici mai alaka da kungiyar IS masu ikirarin jiharadi.
Wasu mata su biyu sun daga hanuwansu suna addua a wajen ginin coci.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu mata na addua a bakin cocin Orthodox ta Habasha a Sudan a ranar Lahadi, waɗanda suka tserewa rikici tsakanin gwamnati da mayakan yankin Tigray a Ethiopia...
Wani badakare na musaman yana tafiya ta gaban wata katanga da harsashi ya bubbula.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Alhamis wani soja na sauri ta jikin wata katanga da harsashi ya huda a kauyen Bisober da ke yankin Tigray.
Mutane na ta ihu a cikin motar safa wani kuma na rike da ganye ya leko ta taga.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan shugaban kasar Jamhuriyar dimokradiyyar Congo na murna bayan samun labarin yanke kawance jam'iyarsu da ta tsohon shugaban ƙasar Joseph Kabila.

Dukkanin hotunan akwai masu su.