Babagana Zulum: Gwamnan Borno ya gamu da fushin ƴan Twitter kan Buhari

Zulum

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu amfani da Twitter sun ce Gwamna Zulum ya ba su mamaki kan yabon Shugaba Buhari duk da yake sau biyu yana tsallake riiya da baya a lokacin mulkinsa
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya gamu da fushin masu amfani da dandalin Twitter saboda yabon da ya yi wa gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kafofin yada labaran kasar sun ambato Gwamna Zulum yana shaida wa tawagar kungiyar Dattawan Arewa, wadda shugaban kwamitin gudanarwarta, Shehu Malami, ya jagoranta zuwa Maiduguri, cewa an samu ingantuwar tsaro a karkashin jagorancin Shugaba Buhari.

A cewar gwamnan, idan aka yi la'akari da halin tsaron da kananan hukumomin jihar 27 suke ciki tun daga 2011 zuwa yanzu, za a iya cewa gwamnatin Buhari ta fi wadanda suka gabace ta a yanayin wanzar da tsaro.

"Alal misali, ba kamar yadda lamura suke kafin zuwan Shugaba Buhari ba lokacin da wasu kananan hukumomi suka kasance wuraren da ba a isa a je ba, yanzu akwai mutane da ke samun jagorancin sarakunan gargajiyarsu a Bama, Gwoza, Askira-Uba, Dikwa, Ngala, Monguno, Kukawa, Damboa, Konduga, da Mafa, dukkansu babu wanda ya isa ya je can a baya ba wai maganar zama ba. An kori dukkan sarakunanmu.

"A yanzu, abubuwa na komawa yadda ya kamata a Bama da Askira-Uba da Damboa da Gwoza da ma sauran garuruwa. Al'amura na komawa daidai a Baga. Kafin zuwan Buhari babu wanda ya isa ya je garuruwan nan. Hasali ma, babu wanda ya isa ya yi tafiyar kilomita kadan a wajen Maiduguri," a cewar Zulum.

Sai dai gwamnan ya ce dabi'ar dan Adam ce ya mayar da hankalin kan halin da yake ciki maimakon tuna abin da ya faru a baya, yana mai cewa mutane na ci gaba da nuna kwarin gwiwar ganin an magance rashin tsaron da ya addabi yankin.

Martanin ƴan Twitter

Sai dai da dama daga cikin masu amfani da shafin Twitter sun soki wadannan kalaman da Gwamna Zulum ya yi, suna masu cewa maganar da ya yi ba ta da kanshin gaskiya.

Hasali ma, sun bayyana cewa shi kansa gwamnan misali ne na ci gaba da tabarbarewar tsaron da ke faruwa a karkashin mulkin Shugaba Buhari domin kuwa sau biyu ana yunkurin kashe shi.

Ameena Usman ta wallafa wani bidiyo na sojoji suna bayyana wa gwamnan fargabar zuwa Baga saboda rashin tsaro amma kuma "ya ce gwamnati ta yi kokari sosai wajen yaki da Boko Haram."

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Shi ma Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar ya ga baiken gwamnan na Borno inda ya ce: "Ba kare Jonathan nake yi ba amma dai lokacin mulkinsa Boko Haram ba ta da karfin kai hari kan gwamna mai-ci kamar yanzu, amma Zulum wanda sau biyu yana tsallake rijiya da baya kan harin da Boko haram ta kai masa a wannan shekarar, yanzu yana fada mana cewa Buhari yana aiki tukuru."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Shi kuwa Gatari ya yi kira ga Gwamna Zulum ya daina siyasa ya fito ya fada wa Shugaba Buhari gaskiya.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Sai dai Aihdee Khalifa ya goyi bayan gwamnan yana mai cewa ya fadi gaskiya domin kuwa yanzu an fi samun zaman lafiya a Maiduguri fiye da a lokutan baya.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4