Andhra Pradesh: Ɗaruruwan mutane sun kamu da 'baƙuwar cuta' a India

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Aƙalla mutum ɗaya ya mutu sannan an kwantar da mutum 227 a asibiti sakamakon kamuwa da wata cuta da ba a san ta ba a jihar Andhra Pradesh da ke kudancin India.

Mutanen da suka kamu da cutar suna nuna alamomi kamar su jiri da kuma suma, a cewar likitoci.

Jami'ai suna gudanar da bincike kan abin da ya haddasa wannan cuta, wadda ta mamaye garin Eluru a ƙarshen mako.

Lamarin na faru ne a yayin da ƙasar India ke ci gaba da fama da cutar korona, wadda take ta biyu a cikin ƙasashen da suka fi kamuwa da ita.

Andhra Pradesh nacikin jihohin da suka fi fama da cutar korona - inda mutum fiye da mutum 800,000 suka harbu da ita, kuma ita ce jiha ta uku da ta fi fama da cutar.

Sai dai da alama ba Covid-19 ta yi sanadin kwantar da mutanen a asibiti ba a ƙarshen mako. Ministan kiwon lafiyar jihar, Alla Kali Krishna Srinivas, ya ce gwajin da aka yi wa marasa lafiyar ya nuna cewa ba sa ɗauke da cutar korona.

"Mutanen da suk kamu da cutar, musamman ƙananan yara, sun riƙa haraswa bayan sun yi ƙarafin cewa idanunsu suna yi musu zafi. Wasu daga cikinsu sun suma," wani likita a asibitin gwamnati na Eluru ya shaida wa jaridar The Indian Express.

An sallami mutum 70 daga asibiti, yayin da ake ci gaba da duba lafiyar mutum 157, a cewar jami'ai.

Wani minista a jihar, Jaganmohan Reddy, ya ce za a tura tawagar likitoci Eluru domin gudanar da bincike kan abin da ya yi sanadin ɓullar. Ana sa ran shi kansa Mr Reddy zai ziyarci garin inda zai gana da marasa lafiya da iyalansu.

Mr Srinivas ya ƙara da cewa an ɗauki samfur na jinin mutanen kuma bai nuna wata shaida cewa ƙwayar cutar bairos ce ta harbe su.

"Jami'anmu da suka ziyarci marasa lafiyar sun gano cewa cutar ba ta da nasaba da shan gurɓataccen ruwa ko shaƙar gurɓatacciyar iskar, " in ji shi. "Wannan baƙuwar cuta ce kuma gwajin kimiyya ne kawai zai tabbatar da wacce ce."

Sai dai jam'iyyar hamayya ta Telugu Desam Party ta yi kira a gudanar da bincike kan lamarin, tana mai cewa gurɓataccen ruwa ne ya haddasa ta.