Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rashin tsaro: 'Katsinawa na guduwa Kaduna su kwana saboda firgici'
Rahotanni daga Jihar Katsina na cewa wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe mutum bakwai cikin kwana uku a yankin ƙaramar ƙukumar Sabuwa ta jihar.
Ɗan majalisar jihar da ke wakiltar Ƙaramar Hukumar Sabuwa, Ibrahim Ɗanjuma Machika, ya shaida cewa an kashe mutanen ne tsakanin Tashar Bawa zuwa Ɗan Kolo da ke yankin.
Ya bayyana cewa mutum biyu daga cikin waɗanda aka kashe ba 'yan yankin ba ne, "domin an kashe su ne yayin da suke tafiya a cikin irin motar Ɗangote, sauran biyar ɗin kuma asalin 'yan yankin ne, kuma tuni aka yi musu jana'iza".
Honourable Ɗanjuma ya shaida cewa babban abin da ya tayar masa da hankali kan wannan harin, shi ne wata mata da goyonta da aka kashe.
Ya bayyana cewa rashin tsaron da ke addabar yankin ya kai ga cewa mutanen da ke a garin Tashar Bawa ba sa iya kwana cikin garin.
Mun tuntuɓi mai magana da yawun 'yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah domin jin ƙarin bayani kan lamarin, sai dai ya ce ba shi da masaniya kan adadin da aka kashe inda ya yi alƙawarin sake kiranmu domin ba mu bayani.
Haka kuma, a garin Gwaram ma na ƙaramar hukumar Talatar Mafara, wasu maharan sun kashe wani dagaci, suka kuma tafi da mutum takwas.
Yankin arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin yankunan da rashin tsaro ya fi addaba inda ko a 'yan kwanakin nan sai da aka bayar da rahoton cewa rashin tsaron ya tilasta wa jama'ar wasu garuruwa shida na jihar Zamfara tsere wa zuwa jihar Kebbi, bayan harin da wasu 'yan bindiga sun kai masu, suka kashe mutum biyar, kuma suka yi awon gaba da wasu biyar, sannan suka shiga ƙona amfanin gona.
A yankin arewa maso gabashin ƙasar kuma, 'yan ƙungiyar Boko Haram ne ke ci gaba da cin karensu babu babbaka, inda a makon da ya gabata aka zarge su da kai wani hari inda suka yi wa wasu manoma 43 yankan rago.