Ƙayatattun hotunan Afirka na mako: 20 - 26 Nuwamban 2020

An wallafa

Ga wasu zaɓaɓɓun hotunan wasu abubuwan da suka faru a wasu sassan Afirka amakon da ya gabata:

Ethiopian refugees who fled fighting in Tigray province play volleyball at the Um Raquba camp in Sudan's eastern Gedaref province, on November 21, 2020.

Asalin hoton, ASHRAF SHAZLY

Bayanan hoto, A ranar Asabar wasu ƴan ƙasar Habasha da suka tsere saboda yaƙin yankin Tigray suna wasan ƙwallon volley gabanin faɗuwar rana a sansanin ƴan gudun hijira na Um Raquba a Sudan....
A woman stands in a metal sheet room that was damaged by shelling, in Humera, Ethiopia, on November 22, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ... a ranar Lahadi a can yankin Tigray, wata mata na kallon hasken rana ta jikin ɓular rufin kwanon da ke ɗakinta a gidanta da ke yankin Humera.
A protester throws a teargas can back at the police during the opposition Economic Freedom Fighters party"s protest against alleged racism outside Brackenfell High School in Cape Town, South Africa, November 20, 2020.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Juma'a hayaƙi mai sa hawaye ya cika sararin samaniya, a yayin da wani mai zanga-zangar adawa da rahotannin wariyar launin fata a wata makarantar sakandare a birnin Cape Town na Afirka Ta Kudu shi ma ya jefi ƴan sandan da wani abu.
Altar servers are seen during a procession before the liturgy in the occasion of the National Pilgrimage in Kita on November 22, 2020. - Since 1966, when the bishops of Mali decided to make Kita the site of a National Pilgrimage, the faithfuls made the journey to the holy sanctuary of Kita where the statue venerated as Notre Dame de Mali is situated. The central theme of this year's gathering is reconciliation of Mali and the freedom of Sister Gloria, kidnapped three years before in Sikasso.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Lahadi ta kasance wata rana ta ibada a Mali, yayin da wasu mabiya addinin kirista suka fara wani tattaki na ibadar ƙasa a Kita...
Catholics faithful are seen praying at the Virgin Mary in the church of Kita during the National Pilgrimage on November 22, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ... Mabiyan ɗariƙar Katolika suna wannan tattaki duk shekara zuwa wajen bauta a Kita, inda suke yin addu'a a gaban gunkin "Our Lady" a Mali.
1px transparent line
Ugandan musician turned politician Robert Kyagulanyi (up,L), also known as Bobi Wine, speaks to supporters on a car roof as an armed man stands, during his presidential rally in Fort Portal on November 23, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Washegari wani mawaƙi a Uganda da ya tsaya takarar shugaban ƙasa ya tsaya a kan motarsa don yi wa taron kamfe ɗinsa bayani.
An electoral commission official holds a ballot paper during vote counting at a polling station during Burkina Faso's presidential and legislative elections, on November 22, 2020 in Ouagadougou.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Lahadi an ƙirga ƙuri'u a zaɓukan Burkina Faso.
A volunteer is examined by Cira 3, a remote-controlled robot that runs tests on suspected coronavirus disease (COVID-19) patients to limit the human exposure to the virus, amid a second wave of infections in Tanta, Egypt, November 18, 2020. Picture taken November 18, 2020.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani butum-butumi yana yi wa wani mara lafiya gwajin cutar korona a Tanta da ke Masar a ranar Juma'a.
A woman points out from a house in Gondar, Ethiopia, on November 23, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Can idan muka sake koma wa Habasha kuwa, a ranar Litinin da yamma rana ta haske gidaje a Gondar a Amhara, yankin da ke kusa da Tigray, inda ake gwabza yaƙi.
A man seats in front of a shop selling mirrors and paintings in Gondar, Ethiopia, on November 23, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ... can kuwa a Gondar, wani mutum na sayar da madubai da hotunan zane-zane.
Ethiopian refugees who fled the fighting in the Tigray region gather on the banks of a border river with Sudan, in the Hamdayit area of Sudan's eastern Kassala state, on November 22, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A yayin da rayuwa ke ci gaba da gudana yadda aka saba a wasu sassan Habasha, abubuwa sun rikice wa dubban mutanen da ke tsere wa faɗan da ake yi a Tigray, nan wasun su ne a kusa da kogin da ke iyakar ƙasar da Sudan a ranar Lahadin da ta gabata.

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka.