Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muhawarar majalisar Birtaniya kan EndSARS ta ja hankalin ƴan Najeriya
Muhawarar da majalisar Birtaniya ta yi kan rikicin EndSARS ta ja hankalin ƴan Najeriya musamman batutuwan da aka tattauna a zauren majalisar.
Ƴan majalisar sun yi muhawara ne a ranar Litinin kan wata takardar koke da mutum fiye da dubu 220 suka sanya wa hannu da ke neman Birtaniya ta ɗauki mataki kan zargin kashe masu zanga-zangar a Najeriya.
Ƴan majalisar ta Birtaniyar sun amince cewa ya kamata gwamnatin ƙasar ta dubi yiwuwar sanya wa jami'an Najeriya takunkumin karya tattalin arziki waɗanda ke da hannu a buɗe wa masu zanga-zangar EndSARS wuta.
Sai dai wannan mataki na majalisar ba tilas ne gwamnatin Birtaniya ta yi aiki da shi ba.
Hukumomin Najeriya dai na ci gaba da musanta cewa jami'an tsaro sun buɗe wuta kan masu zanga-zangar lumana ta adawa da zargin cin zalin ƴan sanda ta EndSARs.
Sai dai batun da yanzu ya fi jan hakalin ƴan Najeriya shi ne zargin rashawa da ɗaya daga cikin ƴan majalisar Birtaniya ya yi wa tsohon shugaban sojan Najeriya Janar Yakubu Gowon da ya mulki Najeriya tsakanin 1966 zuwa 1975.
Majalisar Birtaniya ta yi zargin cewa, "Yakubu Gowon ya gudu zuwa Birtaniya, da kuɗin da aka wawushe daga Babban Bankin Najeriya."
An yi ta yawo da bidiyon ɗan majalisar da ya yi zargin a shafukan sada zumunta musamman Twitter, inda kuma ya janyo muhawara tsakanin ƴan Najeriya - wasu na bayyana girman matsalar rashawa a Najeriya wasu kuma na musanta zargin da aka yi wa tsohon shugaban sojan na Najeriya.
Wasu kuma sun yi kira ga tsohon shugaban ya fito ya yi magana game da zargin.
@jeffphilips1 ya bayyana shakku game da zargin inda ya yi tambayar cewa "yaushe Gowon ya kwashi rabin kudin CBN zuwa Birtaniya? Ina fatan lauyoyinsa sun fara nazarin mayar da martani."
@Robert66096201 mamaki ya yi inda ya ce "Gowon da ake gani a matsayin gwarzo a ƙasar ya wawushe rabin kuɗin CBN"
@cchukudebelu ya ce "Ban yarda ba a ce "Gowon ya saci rabin kuɗin CBN". Gowon ɗalibi ne a Biritaniya a lokacin kamar mahaifina. Ya yi rayuwar hankali."
@henryshield ya ce ya kamata Janar Gowon ya fito ya yi bayani game da zargin da ɗan majalisar Birtaniya ya yi a kansa.
Majalisar Birtaniya kan EndSARS
Majalisar ta kaɗa ƙuri'ar amincewar ɗaukar matakin takunkumi kan jami'an Najeriya da ke da hannu a yin amfani da ƙarfi kan masu zanga-zangar EndSARS a watan jiya.
Majalisar Birtaniya ta ce takunkumi kan Najeriya zai haifar da illa ga ƴan ƙasa, don haka sun yi kira da a gudanar da bincike kan hakkin ɗan Adam da aka keta da kuma neman gwamnatin Birtaniya ta ɗauki matakin takunkumi kan jami'an Najeriya da ke da hannu a harbin masu zanga-zanga a Legas.
Ƴan majalisar sun sha ambaton yadda sojoji suka yi amfani da ƙarfi a kan masu zanga-zanga a Lekki Tollgate da ke Legas.
Sun kuma yi Allah wadai da matakin rufe asusun wasu shugabannin zanga-zangar tare da jaddada cewa ƴancin yin zanga-zanga wani muhimmin ɓangare ne a mulkin dimokraɗiyya.
Wasu daga cikin ƴan majalisar sun tabo batun rawar da Ingila ta taka wajen horar da jami'an tsaron Najeriya da kuma sayar da makamai ga kasar.
Wani ɗan majalisar wakilai da ke magana a madadin ministan Birtaniya a Afirka ya yi maraba da shawarar da Najeriya ta yanke na bincikar zargin take haƙƙi da kuma rusa rundunar ƴan sanda ta musamman - ɓangaren da ke yaƙi da fashi da makami.
Amma ba tare da maraba da kuɗurin sanya takunkumin ba, dan majalisar ya ce Biritaniya za ta ci gaba da matsawa gwamnatin Najeriya lamba ta mutunta ƴancin ɗan adam.