Me ya sa aka fi fifita mawaƙan Hausa na zamani a kan na gargajiya?

Masu rawa
An wallafa

Mawaƙan Hausa na gargajiya sun koka kan yadda ake yi wa maroƙa da mawaƙan Hausa na gargajiya rikon sakainar kashi a yanzu.

Mawakan sun ce irin kallon rainin da ake yi wa waƙoƙin Hausa na gargajiya da kuma maroƙa shi ke kashe sana'ar waƙoƙin gargajiya.

Ɗaya daga cikin 'ya'yan marigayi Alhaji Musa Ɗan-kwairo, wanda ake kira Alhaji Ibrahim Musa Ɗankwairo, ya shaida wa BBC cewa sarakunan gargajiya sun watsar da makaɗa abin da ya suka fada cikin wahala, yana mai cewa ba a kula da su kamar a baya, dalilin da ya jefa sana'ar cikin mawuyacin yanayi.

Ya ce: "Da makaɗi har alfahari ya ke a ce shi ne sarkin makaɗan kaza-kaza na gari kaza saboda ana ɗauke masa komai nasa, amma a yanzu an koma kan mawaƙa na zamani masu yawo da mata sannan su shiga studio su buga waƙa, su ake dauka da daraja".

Mawaƙin ya ce wannan dalili ne ya sa su ma suka sanya 'ya'yansu a makarantun boko saboda su tafi da yadda zamani ya zo da shi.

Alhaji Ibrahim Musa Ɗankwairo ya kara da cewa: "Idan aka yi wasa nan gaba sai an nemi makaɗa da mawaƙan Hausa na gargajiya an rasa saboda yadda aka yi musu riƙon sakainar kashi".

"Raina yana ɓaci saboda a lokacin da muke ƙanana sarakuna ne masu yin alheri, su ne za su ba wa mawaki ko makaɗi kuɗi ko mota ko kuma su kai mutum Makka, kai komai da komai suke maka, amma a yanzu sai a yi naɗin sarauta ka ga an ba wa makaɗin da zai shiga studio ya buga waka in dai ya zo da mata miliyan guda, amma kai an dauko dubu ashirin da biyar da riga biyu an baka," in ji shi.

Shata

An yi watsi da mawaƙan gargajiya shi ya sa na ajiye waƙa na daina yi saboda bani da ra'ayi, a cewarsa.

Alhaji Ibrahim Musa Ɗankwairo ya ce idan ka ga mutum ba ya cikin sukuni da jin daɗi to makaɗin gargajiya ne saboda yadda sarakunan gargajiya suka yi watsi da su.

A cewarsa:"Mu mawaƙa da makaɗan gargajiya mun gano cewa ai boko ke sa ka zamo wani abu, to wallahi sai an wayi gari ba mai yadda ɗansa ya dawo yana wannan sana'a saboda babu ci gaba a cikinta".