Kayatattun hotunan Afirka na wannan makon: Daga ranar 13 - 19 ga watan Nuwamba 2020

An wallafa

Zaɓaɓɓun hotunan abubuwan da suka faru a Afirka na wannan makon.

Ana yi wa wata budurwa a Kenya kwalliya gabanin aurenta da za a daura ranar Asabar

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ana yi wa wata budurwa a Kenya kwalliya gabanin aurenta da za a daura ranar Asabar
A ranar ce kuma a kasar Masar, wannan masanin ilimin kufai yana duba wata tsohuwar gawa da aka adana

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar ce kuma a kasar Masar, wannan masanin ilimin kufai yana duba wata tsohuwar gawa da aka adana...
An gano tsoffin gawarwaki a cikin akwatunansu a Saqqara

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An gano tsoffin gawarwaki a cikin akwatunansu a Saqqara
Masunta biyu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masunta a gabar tekun Fish Hoek da ke Cape Town sun baza komarsu ranar Talata. Suna janye ta a yammacin kowacce rana sannan su koma washegari da safe
Robert Kyagulanyi, wanda aka fi sani da Bobi Wine

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An kama dan kasar shugaban Uganda na jam'iyyar adawa Bobi Wine lokacin yakin neman zabe ranar Laraba. Magoya bayansa da suka yi fushi sun gudanar da zanga-zanga, lamarin da ya yi sandin mutuwar akalla mutum 16. Sauran 'yan takarar jam'iyyun adawa sun dakatar da yakin neman zabensu domin nuna bijirewarsu kan kama shi
Wannan mutumin yana gina matsuguni a Um Raquba da ke Sudan bayan ya tsere daga rikicin da ake yi tsakanin gwamnatin tarayyar Ethiopia da dakarun lardin Tigray ranar Lahadi...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan mutumin yana gina matsuguni a sansanin 'yan gudun hijira Um Raquba da ke Sudan bayan ya tsere daga rikicin da ake yi tsakanin gwamnatin tarayyar Ethiopia da dakarun lardin Tigray ranar Lahadi...
Wadannan yaran na cikin dubban mutanen da ke zaune a sansanin...

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wadannan yaran na cikin dubban mutanen da ke zaune a sansanin...
Hundreds of people walk next to and gather by the banks of the Setit River on the Sudan-Ethiopia border, on 14 November.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Rahotanni sun ce an kashe daruruwan mutane a yankin Tigray kuma akalla mutum 30,000 sun tsallaka iyaka zuwa Sudan.
A Senegal ranar Asabar, Aminata Gueye tana nuna hoton danta mai shekara 24 Mohamed, wanda ya mutu a cikin teku a yayin da yake kokarin zuwa Tsiriban Canary da ke Sifaniya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A Senegal ranar Asabar, Aminata Gueye tana nuna hoton danta mai shekara 24 Mohamed, wanda ya mutu a cikin teku a yayin da yake kokarin zuwa Tsiriban Canary da ke Sifaniya
Ranar Litinin, mata 'yan makaranta a Zimbabwe suna kallon littafi tare

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Litinin, mata 'yan makaranta a Zimbabwe suna kallon littafi tare

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.