Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnan Ebonyi ya fice jam'iyyar PDP zuwa APC
Gwamnan jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya David Umahi, ya sanar da sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC ta shugaba Buhari
"Na bar PDP saboda rashin adalci," kamar yadda gwamna Umahi ya tabbatar da labarin ficewarsa ga mutanen Abakaliki babban birnin Ebonyi.
Jam'iyyar PDP ma ta tabbatar da labarin ficewarsa a cikin wata sanarewa da kakakinta Kola Ologbondiyan ya fitar ranar Talata.
PDP ta ce gwamna Umahi ya bar jam'iyyar ne saboda wasu dalilai na ƙashin kansa, kuma a cewar jam'iyyar nan gaba kaɗan ƴan Najeriya za su fahimci dalilansa.
An ta jita-jitar cewa gwamnan zai fice daga PDP, inda wasu ke cewa yana shirin fitowa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Jam'iyyar APC ta yi maraba da babban kamun da ta yi a shafinta na Twitter inda ta ce "Barka da zuwa Gwamna David Nweze Umahi, Yanzu Ebonyi ta APC ce."
Sanarwar da PDP ta fitar ta ce "Muna godiya ga Gwamna Umahi ga ayyukan da ya yi wa mutanen jihar Ebonyi, a matsayin shugaban PDP daga 2003 zuwa 2007, mataimakin gwamnan Ebonyi daga 2007 zuwa 2015 da kuma wa'adi biyu da aka zaɓe shi matsayin gwamna ƙarkashin PDP daga 2015 zuwa yanzu."
Dalilansa na sauya sheƙa
Daga cikin dalilan da gwamnan na jihar Ebonyi ya bayar na sauya sheƙa zuwa APC, ya ce "Saboda ba ni faɗin wani mugun abu ga shugaba Buhari"
Ya kuma ce yadda mutanen kudu maso gabashi ke goyon bayan jam'iyyar PDP musamman yadda take lashe zaɓe a jihohin yankin guda biyar tun 1998, jam'iyyar ba ta taɓa tsayar da wani ɗan yankin a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ba."