An kori Bayahuden da ya tofa yawu a hoton da aka alaƙanta da 'Annabi Isa'

Hukumar kula da motocin daukar marasa lafiya ta Isra'ila ta yi "matukar Allah-wadai" da abin da mutumin ya aikata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hukumar kula da motocin daukar marasa lafiya ta Isra'ila ta yi "matukar Allah-wadai" da abin da mutumin ya aikata
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

An kori wani jami'in lafiya a Isra'ila daga aiki bayan kamara ta hango shi yana tofa yawu a jikin wani zane da aka alaƙanta da Annabi isa a lokacin da ya ziyarci gidan wasu Kiristoci domin yi musu gwajin cutar korona.

An hango mutumin yana cire takunkumin da ya rufe fuskarsa sannan ya tofa yawu sau uku a hoton da ke rataye a jikin dakin ginin da ya shiga da ke Jaffa na birnin Tel Aviv.

Lokacin da aka kalubalance shi kan abin da ya aikata, mutumin ya yi ikirarin cewa ɗaukar hoto da kuma ajiye shi ani nau'i ne na bautar gumaka da aka haramta a cikin littafin Attaura.

Hukumar kula da motocin daukar marasa lafiya ta Isra'ila, inda yake aiki, ta ce ta yi "matukar Allah-wadai" da abin da mutumin ya aikata.

Ta kara da cewa abin da mutumin ya yi "bai wakilci hukumar" ba inda ta kore shi nan take.

Lamarin ya faru ne ranar Lahadi lokacin da ma'aikacin lafiyar ya je gidan mutanen da zai yi wa gwajin cutar korona - inda dukkan mazaunansa Kiristoci ne, a cewar rahotanni.

Hotunan da kamarorin tsaro suka nada sun nuna ma'aikacin yana cire takunkumin da ke fuskansa da kuma tufafin kariyar da ke jikinsa kafin ya juya sannan ya tofa yawu sau uku a jere.

Daga bisani an gan shi yana sanya takunkuminsa sanna ya yi tafiyarsa.

A yayin da yake barin ginin rukumin gidajen da ya je, ya hadu da wani mazaunin gidajen wanda ya nadi abubuwan da suka faru a wayarsa ta salula.

Lokacin da mutumin ya tambayi ma'aikacin ko me ya sa ya tofa yawu a jikin zanen hoton Annabi Isa, ai ya ce: "A Yahudancin wannan bakon abu ne."

Bidiyon ya nuna mazaunin rukunin gidajen yana shaida wa ma'aikacin lafiyar cewa: "Ka tofa yawu a hotunana, a abin da muka yi imani da shi, kuma a gaban kyamara. Me ya sa ka yi haka?"

Ma'aikacin lafiyar ya bayar da amsa cewa : "A littafin Attaura an rubuta cewa a yi bakin kokari wajen yin watsi da bidi'a," sannna ya yi korafi ga mazaunin rukunin gidajen cewa bai sanya takunkumi ba.

An kai batun ga ma'aikatar da mutumin yake yi wa aii inda ta kore shi.

A wani sako da ta wallafa a Twitter, Hukumar kula da motocin daukar marasa lafiya ta Isra'ila ta ce ta yi "Allah wadai" da abin da ya faru, inda ta kara da cewa tana aiki da mutanen da ke da mabambantan addinai.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Isra'ila na cikin kasashen da suka fi fama da cutar korona kuma yanzu ne take farafadowa daga cikin dokar kulle karo na biyu da aka sanya.