Lagos: 'Yan sanda sun kama mutum 720 da makamai da tabar wiwi

An wallafa

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta tabbatar da kama mutum 720 inda aka same su da abubuwa daban-daban da suka haɗa da bindigogi ƙirar gargajejiya da harsasai, da tabar wiwi da wata hoda da ake zaton hodar ibilis ce.

A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan reshen jihar Legas SP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta bayyana cewa an samu kama waɗannan mutane ne yayin wani samame da aka kai da safiyar Lahadi a wasu wurare da ake zaton maɓuyar masu laifuka ne a sassa 14 a jihar.

Sanarwar ta bayyana cewa wasu daga cikin kayayyakin da aka ƙwato ana zaton an sato su ne yayin hare-hare da aka kai na fasa shaguna a lokacin zanga-zangar EndSars a watan Oktoba.

Tuni dai kwamishinan 'yan sandan jihar Hakeem Odumosu ya bayar da umarnin ƙaddamar da bincike kan waɗanda aka kama domin gurfanar da su gaban kotu.

Ya kuma buƙaci waɗanda aka yi wa sata a lokacin zanga-zangar EndSars da su zo su duba kayayyakinsu da kuma shaidar cewa mallakarsu ne.

Ya kuma yaba wa 'yan sandan jihar bisa jajircewarsu wurin wannan samamen da suka kai, inda kuma ya buƙace su da su kasance cikin ko ta kwana domin aiwatar da irin wannan samamen a nan gaba.

A kwanakin baya ne dai rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa masu zanga-zangar EndSars sun kashe 'yan sanda 22 da raunata da dama daga cikinsu, kuma akasarin 'yan sandan da aka raunata na cikin matsanancin hali.

Haka kuma rundunar ta bayyana cewa an ƙona ofisoshinsu 205 yayin zanga-zangar.