EndSAR; Za mu bi kadin 'yan arewa da aka kashe a rikicin da ya faru

Shugabannin al'ummar Igbo mazauna arewacin Najeriya sun yi alwashin hada-gwiwa da gamayyar ƙungiyoyin farar hula da ke lardin wajen bin kadun ƴan arewa mazauna kudu da suka rasu da wadanda suka yi asarar dukiya a rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar EndSARS.
Shugabannin sun ce za su ja hankalin gwamnonin jihohin kudancin ƙasar domin a biya diyya ga wadanda asarar ta shafa.
An yi tattaunawa tsakanin shugabannin al`ummar Ibo daga jihohi goma sha tara da ke arewacin Najeriya da kuma Abuja, babban birnin ƙasar, da shugabannin gamayyar ƙungiyoyin farar-hula da ke arewacin ƙasar.
Tattaunawar ta mayar da hankali a kan rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar da aka yi a ƙasar ta kyamar cin zalin ƴan sanda na rundunar SARS da gwamnati ta soke.
Musamman ma yadda rikicin ya shafi ƴan arewa da ke kudu maso kudu da kudu maso gabas a Najeriya da hanyoyin magance hakan a gaba.
Me gamayyar ƙungiyar farar hular ke cewa?
Shugaban ƙwamitin amintattu na gamayyar ƙungiyoyin farar-hula da ke arewacin Najeriya, Nastura Ashiru Shariff, ya shaida wa BBC cewa asarar da ƴan arewan suka yi ba karama ba ce.
Ya ce, sun tattauna akan yadda ya kamata shugabanni su san cewa idan an samu matsala irin wannan su rinka jan hankalin mutane a kan daina ɗaukar doka a hannunsu.
Sannan kuma ya kamata shugabannin al'ummar Igbon su zauna su tattauna a kan irin ɓarnar da aka yiwa ƴan arewa mazauna can domin su biya su diyya, in ji Nastura Shariff.
Ya ce "asarar da ƴan arewa suka yi ba karama ce domin a jihar Aba ta jihar Abia kadai ƴan arewan sun yi asarar fiye da naira biliyan ɗaya".
Haka kuma aka rinka tare motocin da ke tafiya a kan tituna wanda aka san na ƴan arewa ne ana kashe su. in ji Nastura.
Me shugabannin al'ummar Igbo suka tsayar?
Shugaban al`ummar Igbo mazauna arewacin Najeriya, Chief Chikezie Nwogu, ya ce sun yi tir da abin da ya faru, kuma da su za a bi kadun ƴan arewa da suka yi asara a kudancin ƙasar.
Ya ce abin da aka yi ba a kyauta ba, mun rubuta wasika cewa muna son ganin gwamna don mu tattauna a kan yadda za a biya ƴan arewa diyya.
Karin haske
A makon da ya wuce gamayyar ƙungiyoyin farar-hula da ke arewacin Najeriyar ta yi zargin cewa gwamnatocin jihohin kudancin ƙasar, da takwarorinsu na arewa, duka ba sa maganar ƴan arewa da rikicin EndSARS din ya shafa.
Gamayar ta ce ko saka su a cikin wadanda suke nema a biya diyyar asarar da suka yi ba a yi. Wannan ya sa gamayyar ta yi alwashin tsaya musu.











