Hotunan Afrika na wannan makon tsakanin 6-12 ga watan Nuwamba 2020

Wani mutum yana tura keke a tsakiyar filawar bishiyoyi jacaranda

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mutum yana tura keke a tsakiyar furannin bishiyoyin Jacaranda da ke Johannesburg a Afrika ta Kudu ranar Juma'a
An wallafa
Wani mutum na dauke da kujera a wajen wata makaranta, wanda aka yi zanensa a jikin bango.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Washegari a Alkahira babban birnin Masar, mutane na gyara kujeru bayan sanar da amfani da makarantu a matsayin rumfunan zaɓe a zaɓen 'yan majalisar dokokin ƙasar
Wani kwararren hawa kumbo dauke da wani ɗan yawon buɗe ido

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu mutane masu yawo a sama da kumbo, sun ƙure saman dala da ke Giza a Masar
1px transparent line
Wani mai zane tsaye akan tsani, yayin da yake zana tafin hannun da ke son kama wasu fararen tantabaru

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani mai zane "da ke alamta zaman lafiya" a Bingerville, a Ivory Coast a ranar Asabar, bayan 'yan adawar ƙasar sun yi kiran a ƙaurace wa zaben shugaban ƙasar saboda tsayawa takarar shugaban a karo na uku
Wani mata shi a lokacin yaƙin neman zaɓe

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Lokacin yaƙin neman zaɓe na ƙaratowa a Burkina Faso, inda wannan magoyin bayan shugaban kasar ke yi masa fatan nasara da wannan rubutun da aka yi a jikinsa
Wata mata zaune cikin murmushi a kan bishiya tana neman a daina sare bishiyoyi ta na cewa muna bukatarsu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Laraba, Phyllis Wamaitha na zaune kan wata bishiya da ta dauki shekaru a Kenya, wadda ke rajin kare muhalli nata cewa bishiyoyi su ma suna da rai, mu daina sare su saboda gina tituna.
Wata yarinya na tsallae ta cikin ruwa kusa da gidansu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A dai Kenya wata yarinya na tsallake ruwa bayan kogin Naivisha ya cika ya tsallako cikin gari, ya raba daruruwan mutane da muhallansu a ranar Asabar...
Wasu bishiyoyi da ke tsakiyar ruwa ganyayensu duk sun kaɗe

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kafafen yaɗa labarai na cikin gida na cewa hakan ya faru ne sakamakon sauyin yanayi

Dukkan hotuna suna da hakkin mallaka