Bayanan hoto, Ranar Litinin 9 ga watan Nuwamba ne ake bikin bayar da sandar girma ga Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, sabon sarkin Zazzau
An wallafa
Asalin hoton, Twitter/@GovKaduna
Bayanan hoto, Gwamna Nasir El-Rufai ne ya mika wa Sarkin sandar girma
Bayanan hoto, A watan jiya ne gwamnatin Kaduna ta nada Ambasada Ahmed Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19 bayan rasuwar Sarki Alhaji Shehu Idris, wanda ya kwashe fiye da shekara 40 a gadon sarauta
Bayanan hoto, Dumbin mutane ne suka halarci wajen biki, ciki har da Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Abubakar na III da Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi...
Bayanan hoto, ...Jama'ar da suka halarci bikin nadin sun fito daga sassa daban-daban na kasar
Bayanan hoto, Makada da mawaka sun baje kolinsu a wajen bikin
Bayanan hoto, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Abubakar na III lokacin da yake isa wajen bikin bayar da sandan girma ga Sarki Ahmed Nuhu Bamalli
Bayanan hoto, Mahalarta bikin sun jinjina wa gwamnati bisa zabin da ta yi
Bayanan hoto, Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi lokacin da ya isa wajen bikin bayar da sandar mulki ga Sarkin Zazzau
Bayanan hoto, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau kuma jakadan Najeriya a kasar Thailand kafin nadinsa a matsayin sarki