Bidiyo: Rikicin sarauta abu ne na cikin gida da za mu daidaita tsakaninmu - Sarkin Zazzau
An wallafa
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ranar Litinin 9 ga watan Nuwamba ce aka shirya za a ba sabon Sarkin Zazzau Jakada Ahmad Nuhu Bamalli sandar girma.
Bayar da sandar girma na ɗaya daga cikin bukukuwan da ake yi yayin da masarauta ta samu sabon sarki bayan gwamna ya tabbatar da shi.
BBC ta sami damar tattauna ta musamman da Sarki Ahmad Nuhu Bamalli wanda ya shaida ma ta cewa yana fatan ya haɗa kan duka gidajen sarautar Zazzau, kuma ya bayyana dalilin da ya sa suka zaɓi ranar 9 ga watan Nuwamba a matsayin ranar bayar da sandar girman.