Isra'ila ta rushe gidajen Falasɗinawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah-wadai da abin da Isra'ila ta yi, wanda ta ce shi ne rusau mafi girma da aka yi wa gidajen Falasɗinawa a Yamma da Gaɓar Kogin Jordan cikin sama da shekara 10.

Rusau ɗin ya raba mutum 73 da muhallansu ciki har da yara 41, bayan rushe inda suke zaune a Beduuin da ke Khirbet Humsa a tsaunukan Jordan, kamar yadda MDD ta ce.

Dakarun Isra'ila sun ce an yi gine-ginen yankin ne ba bisa ƙa'ida ba.

Sai dai MDD ta kira wannan mataki na Isra'ila a matsayin "sanya ƙafa a shure" dokar ƙasa da ƙasa.

Kamar yadda ofishin ba da agaji na MDD Ocha ya bayyana, gine-gine 76 ciki har da gidaje da burtalai da banɗaki da farantan samar da wuta mai amfani da hasken rana - duka aka rushe a yammacin ranar Talata.

Hukumomin Isra'ila sun ce adadin gine-ginen ba su kai haka ba, suna cewa "an gabatar da dokar ne" kan wasu tantuna bakwai da burtalan dabbobi takwas.

Wani bidiyo da hukumar kare hakkin ɗan adam ta Isra'ila ta fitar kan rushe gine-ginen, ya nuna yadda aka yi watsi da kayayyaki kamar gadaje da abin shimfida da kuma sauran kayayyakin gida.

''Wanan ba ƙaramin rashin adalci ba ne,'' kamar yadda wani mazaunin yankin Harb Abu al Kabash ya shaida wa wata jaridar Isra'ila Haaretz0.

"Ba mu san za su zo ba don haka ba mu shirya ba kuma ga shi yanzu muna fama da ruwan sama.

Cikin wata sanarwa da sojojin Isra'ila masu lura da al'amuran mutanen da ke zaune a Yamma da Gaɓar Kogin Jordan ta ce, gine-ginen da aka rushe an gina su ba bisa ƙa'ida ba, kuma a yankin da ba ya rabuwa da faɗace-faɗace, ko ma mu kira shi wani yankin da dakaru ke atisaye a ciki.

Ocha ya ce yankin Khirbet Humsa wanda aka fi sani da Humsa al-Bqaiaa da Larabci, na daya daga cikin yankuna 38 na mutane da da aka keɓe daga inda ake rikici, kuma yake ɗauke da mutane masu rauni a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Ta ƙara da cewa wannan rusau ɗin ya karya ƙa'idar yarjejeniyar dokar ƙasa da kasa da aka cimma a Geneva - wadda za ta ƙare fararen hular da ke zaune a yankunan da aka mamaye.

Isra'ila ta mamaye yankin Yamma da Kogin Jordan ne a lokacin yankin Gabas Ta Tsakiya a 1967.

Ƙarkashin yarjejeniyar da ta biyo baya, aka taƙaita wa Falasɗinawa sashen da za su kasance, yayin da Isra'ila za ta ci gaba da samun cikakken iko da wajen.

Khirbet dai yana wajen yankin da Falasɗinawa ke da iko da shi.