Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dokar kullen wata guda ta fara aiki a Ingila
A yayin da ƙasashen nahiyar turai ke ƙoƙarin takaita yaduwar cutar korona bayan cutar ta ci gaba da yaduwa a zagaye na biyu, Ingila ma ta bi sahun inda dokar kulle ta fara aiki a karo na biyu.
Za dai a shafe tsawon wata guda ana cikin wannan doka kamar yadda Firanministan ƙasar Boris Johnson ya sanar.
Ko da yake a wannan karon akwai wasu muhimman wurare da dokar bata shafa ba kamar makarantu saboda zasu kasance a buɗe.
Wannan doka dai ta shafi wuraren cin abinci da kuma shagunan da bana sayar da muhimman abubuwan amfani ba.
Bayanai sun nuna cewa an samu mutum dari biyar da suka mutu bayan sun kamu da cutar korona a rana a 'yan kwanakin nan a Birtaniya, adadin da aka jima ba a samu ba tun watan Mayun da ya wuce.
A baya Mr Johnson ya yi ta jan kafa wurin daukar irin wannan mataki, to amma a yanzu ya ce ba su da zabi.
To sai dai masu kamfunoni a Ingila sun ce irin yadda bikin Kirsimati ya matse za a gurgunta harkokin kasuwanci za kuma a rasa ayyukan yi.
Ba Birtaniya abin ya tsaya kadai ba, Polanda ma zata rufe gidajen kallo wato sinima da wuraren adana kayan tarihi da kuma mafi yawancin kasuwanni a kasar daga ranar Asabar 7 ga watan Nuwambar, 2020.
Wannan dai ya biyi bayan samun mutum kusan dubu ashirin da hudu da suka kamu da cutar a rana guda a kasar.
Kazalika a an rufe wurare da dama ma a Portugal a ranar Laraba 4 ga watan Nuwambar, 2020.
A bangare guda kuma, a yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben Amurka, adadin wadanda suka kamu da cutar korona a kasar a rana guda ya karu ind aka samu mutum fiye da dubu casa'in da daya.
Ya zuwa yanzu dai an samu mutum kusan miliyan tara da dubu dari biyar da suka kamu da cutar a kasar, inda fiye da dubu dari biyu da talatin da uku kuma suka mutu saboda cutar a kasar.