WAEC: Ga yadda za ku duba sakamakon jarrabawarku

A ranar Litinin 2 ga watan Nuwamban 2020 ne hukumar tsara jarrabawar kammala sakandare ta Afirka Ta Yamma WAEC ta saki sakamakon ɗaliban da suka rubuta jarrabawar ta bana.
Sai dai kuma hukumar ta ce ta riƙe sakamakon ɗalibai 215, 149 daga cikin waɗanda suka rubuta jarrabawar.
Patrick Areghan wanda shi ne shugaban ofishin na Najeriya a wata sanarwa ya ce sun riƙe sakamakon jarrabawar ne bisa zargin satar amsa da ake wa wasu ɗaliban da yi.
Ya ce tuni sun fara bincike kan satar amsar.
Idan kuna cikin waɗanda aka saki sakamakonsu, to ga matakan da za ku bi ku duba.
Babban abin da ake buƙata shi ne ku duba lambar sirri (pin) da wasu jerin lambobi (serial number) da ke kan wani katin shaida na musamman da aka ba ku a lokacin jarrabawar.
Sannan sai ku bi waɗannan matakan:
1. Ku shiga shafin https://www.waecdirect.org wanda shi ne shafin WAEC na duba jarrabawar.
2. Ku shigar da lambarku ta jarrabawar WAEC a gurbin da ake buƙata.
3. Ku zaɓi shekarar jarrabawarku
4. Ku zaɓi tsarin jarrabawarkuku wanda shi ne inda aka rubuta "school candidate result".
5. Daga nan sai ku shigar da lamar nan ta jikin katin (Card Serial Number).
6. Bayan nan sai ku sanya lambar pin ɗin katin.
7. A ƙarshe sai ku latsa "Submit" don samun sakamakon jarrabawarku ta WAEC ta shekarar 2020.











