Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ɗan Tunisia ne ya kashe mutum uku a Faransa
Mahukunta a Faransa sun gano wane ne mutumin da ya kai harin wuƙa a birnin Nice na ƙasar, tare da kashe wasu mutum uku a ranar Alhamis.
Mutumin mai shekara 21, wanda aka bayyana sunansa da Brahim Awisawi, na kwance a wani asibiti cikin yanayi mai tsanani bayan harbi da ƴan sanda suka yi masa.
Masu bincike a Italiya sun ce ya isa tsibirin Lampedusa a matsayin dan cirani a watan da ya gabata, kuma bayan cike kwanakin keɓe kai an bashi damar ci gaba da balaguronsa.
Shugaba Emmanuel Macron, wanda ya ziyarci birnin na Nice ya ce irin wannan hari ba abu ne da Faransa za ta lamuncewa ba.
Mutumin da ake zargi ya isa Nice ne ta jirgin kasa kuma baya ɗauke da takardu, illa takardar agaji ta Red Cross daga Italiya, sai kuma wuƙaƙe uku, da wayoyi biyu.
A wani jawabi da shugaban na Faransa ya yi a ranar Alhamis, ya yi tur da kisan mutanen uku, ya kuma ce Faransa na fuskantar suka saboda dabi'unta kuma ba za ta taba mika wuya ga ta'addanci ba.
Shugaban kasar zai ninka adadin sojojin da ke ba da tsaro a wuraren taron jama'a domin kare majami'u da makarantu.
Ƙasashe da dama a faɗin duniya tuni suka fara batun ƙaurace wa kayayyakin Faransa, llamarin da zai iya jefa tattallin arziƙin ƙasar cikin wani hali.
Hakan ya sa a wannan makon ƙasar ta Faransa ta buƙaci kasashen Gabas Ta Tsakiya da ka da su amince da kiraye-kirayen ƙaurace wa sayen kayayyakinta.