Ahmed Nuhu Bamalli: An soma shari'a kan ƙarar da aka kai sabon sarkin Zazzau

Asalin hoton, Zazzau Emirate
Wata kotu a birnin Zariya da ke jihar Kadunan Najeriya ta soma sauraren ƙarar da aka kai sabon Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli.
Alhaji Bashari Aminu (Iyan Zazzau) ne ya shigar da ƙarar a Babbar Kotun jihar Kaduna da ke Dogarawa Sabon Garin Zariya, inda yake ƙalubalantar naɗin Ahmed Nuhu Bamalli a matayin Sarkin Zazzau.
Alhaji Aminu na cikin mutanen da suka nemi sarautar ta Zazzau.
Ɗaya daga cikin lauyoyin da suka shigar da ƙarar ya tabbatar wa BBC cewa sun gurfanar da Sarkin a kotun mai shari'a Kabir Dabo.
A takardun, an yi ƙarar mutane da dama da suka haɗa da gwamnan jihar Kaduna da Antoni Janar na jihar Kaduna da Majalisar Sarakunan jihar Kaduna da Majalisar Masarautar Zazzau da Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu (Wazirin Zazzau) da Alhaji Umaru Muhammad (Faghazin Zazzau) da Alhaji Muhammad Abbas (Makama Karamin Zazzau).
Sauran su ne Alhaji Dalhatu Kasimu Imam (Limamin Juma'ar Zazzau) da Alhaji Muhammad Sani Aliyu (Limamin Konan Zazzau) da kuma Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.
A makon jiya mun ruwaito cewa ba a shigar da ƙarar ba bayan lauyan da aka yi ikirarin cewa shi ne ya garzaya kotu a madadin Iyan Zazzau, Ustaz Yunus, ya shaida mana cewa bai san komai a kan batun
An ɗaga sauraron shari'ar zuwa 27 ga watan Oktoban 2020.
Waiwaye
A ranar 7 ga watan Oktoba ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da naɗa Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19.
"Alhaji Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan Mallawa cikin shekara 100 da suka gabata, bayan rasuwar kakansa Sarki Dan Sidi a shekarar 1920," a cewar sanarwar da gwamnatin ta fitar.
Sabon sarkin ya fafata da mutane da dama wajen neman saautar, sai dai tuni wasu daga cikinsu irin su Mannir Jafaru (Yariman Zazzau) suka yi mubaya'a a gare shi.
A tattaunawa da manema labarai, ya nuna farin cikinsa matuƙa sakamakon Allah ya ƙaddara cewa wannan sarauta ta dawo gidansu kuma a kansa, amma ya ce duk a rayuwarsa, burinsa shi ne mahaifinsa ya yi sarautar Zazzau ba shi ba.
Ya kuma ce zai gudanar da mulki ba tare da nuna bambanci tsakanin sa da sauran gidajen sarautar da suka fafata wajen neman sarautar ba.
Mai Martaba Ahmad Nuhu Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan Mallawa da ya hau gadon sarauta cikin shekara 100, bayan rasuwar kakansa Sarki Dan Sidi a 1920.
Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau kuma jakadan Najeriya a kasar Thailand kafin nadinsa a matsayin sarki.










