Ahmed Nuhu Bamalli: Da gaske an kai ƙarar sabon Sarkin Zazzau kotu?

Asalin hoton, Zazzau Emirate
Binciken da BBC Hausa ta yi ya gano cewa rahotannin da ke cewa an kai ƙarar sabon sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli kotu domin ƙalubalantar naɗa shi a kan sarauta ba su da ƙamshin gaskiya.
Tun a ƙarshen makon jiya ne aka riƙa yaɗa wasu takardu da ake cewa na ƙarar da Alhaji Bashari Aminu (Iyan Zazzau) ya shigar kan sabon sarkin a wata babbar kotun Kaduna ne.
A takardun, an yi ƙarar mutane da dama da suka haɗa da gwamnan jihar Kaduna, Antoni Janar na jihar Kaduna, Majalisar Sarakunan jihar Kaduna, Majalisar Masarautar Zazzau, Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu (Wazirin Zazzau), Alhaji Umaru Muhammad (Faghazin Zazzau), Alhaji Muhammad Abbas (Makama Karamin Zazzau).
Sauran su ne Alhaji Dalhatu Kasimu Imam ( Limamin Jumu'an Zazzau), Alhaji Muhammad Sani Aliyu (Limamin Konan Zazzau), da kuma Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.
Sai dai takardun shigar da ƙarar da ake ta yaɗawa ba sa ɗauke da kwanan wata da sa hannu ko hatimi na lauyan da ke cikin takardar.

Asalin hoton, OTHER

Asalin hoton, OTHER
Ba mu san da wannan batu ba
Takardun da aka ce na shigar da ƙara ne sun nuna cewa Babban Lauyan Najeriya Ustaz Yunus (SAN) shi ne wanda ya shigar da ƙarar a madadin Alhaji Bashari Aminu (Iyan Zazzau).
Sai dai wakilin BBC Yusuf Tijjani, wanda ya yi tattaki har ofishin lauyan a Kaduna, ya ambato Mr Yunus na cewa ba su shigar da ƙara a madadin Iyan Zazzau ba.
A cewarsa: "Ba mu san komai a kan shigar da ƙarar ba, don haka ba mu ne muka shigar da ita ba idan ma an shigar."
Ya ƙara da cewa ba ya buƙatar yin dogon tsokaci a kan batun tun da babu ƙanshin gaskiya a cikinsa.
A bangare guda, wani makusancin Iyan Zazzau ya tabbatar wa da wakilin namu cewa ba su kai kowa kara kan batun sarautar Zazzau ba kawo yanzu.
Sai dai bai yi ƙarin bayani ba kan ko suna da shirin yin hakan nan gaba.
Waiwaye
A makon jiya ne gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da naɗa Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19.
"Alhaji Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan Mallawa cikin shekara 100 da suka gabata, bayan rasuwar kakansa Sarki Dan Sidi a shekarar 1920," a cewar sanarwar da gwamnatin ta fitar.
Sabon sarkin ya fafata da mutane da dama wajen neman saautar, sai dai tuni wasu daga cikinsu irin su Mannir Jafaru (Yariman Zazzau) suka yi mubaya'a a gare shi.
A tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, ya nuna farin cikinsa matuƙa sakamakon Allah ya ƙaddara cewa wannan sarauta ta dawo gidansu kuma a kansa, amma ya ce duk a rayuwarsa, burinsa shi ne mahaifinsa ya yi sarautar Zazzau ba shi ba.
Ya kuma ce zai gudanar da mulki ba tare da nuna bambanci tsakanin sa da sauran gidajen sarautar da suka fafata wajen neman sarautar ba.
Mai Martaba Ahmad Nuhu Bamalli shi ne sarki na farko daga gidan Mallawa da ya hau gadon Sarauta cikin shekara 100, bayan rasuwar kakansa Sarki Dan Sidi a 1920.
Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau kuma jakadan Najeriya a kasar Thailand kafin nadinsa a matsayin sarki.










