Ƙayatattun hotunan wasu abubuwan da suka faru a Afirka a makon nan: 9-15 ga Oktoban 2020

An wallafa

Ga wasu zaɓaɓɓun hotunan wasu abubuwan da suka faru a Afirka a makon nan:

Two young women pose for a portrait, dressed in robes after collecting their Bachelor degrees in Conakry on October 12, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Litinin dalibai sun karbi shaidar kammala digiri insu a babban birnin Guinea, Conakry...
A man sits in front of campaign posters of President Alpha Conde in Conakry, on October 13, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ...An liƙa fastocin ƴan takara a ko ina a cikin gari domin tuna wa mutane zaɓen shugaban kasa ranar Lahadi inda Alpha Condé zai sake tsayawa takara a karo na uku...
A supporter holds up a painting of main opposition candidate, Cellou Dalein Diallo in Conakry on October 14, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ...Cellou Dalein Diallo zai fafata da Mr Condé, magoya bayansa kamar wannan mutumin, na ɗauke da zanen ɗan takarar tasa sauran magoya baya kuma na buga gangar goyon baya.
A demonstrator stands atop a vehicle and shouts slogans as others carry banners while blocking a road leading to the airport, during a protest over alleged police brutality, in Lagos, Nigeria October 12, 2020.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Litinin wata mai zanga-zanga a Legas ta tsaya a kan mota tana neman a yi wani abu game da zaluncin ƴan sanda a Najeriya...
A demonstrator in underwear carries a hairdryer and a megaphone during a protest over alleged police brutality, in Lagos, Nigeria October 14, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ... kwana ɗaya bayan nan wani mai zanga-zangar a Abuja, babban birnin Najeriyar, shi kuma ya fito da nasa salon don jan hankalin jama'a.
Rickshaw taxis drive past the Salaam Somali Bank in Wadajir district of Mogadishu, Somalia October 14, 2020.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Laraba a Mogadishu na Somaliya, wani mutum na jiran babur mai ƙafa uku su wuce kafin ya tsallaka titi.
Volunteers prepare food parcels before a distribution leaded by the international NGO Gift to the Givers, in Johannesburg CBD, on October 14, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Laraba, wasu masu aikin sa kai a birnin Johannesburg na Afirka Ta Kudu, suna miƙa taimakon abinci ga mutanen da ke cikin yanayin kullen cutar korona.
A schoolgirl wears a face mask as she reads a book inside a classroom at the Olympic Primary School during the partial reopening of schools, after the government scrapped plans to cancel the academic year due to the coronavirus disease (COVID-19) pandemic, in Kibera slums of Nairobi, Kenya October 12, 2020.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Litinin yara a Kenya sun koma makarantu tun bayan rufe su da aka yi a Maris domin rage yaduwar Korona.
A family hold hands as they collect themselves in prayer while taking part in a special mass prayer meeting in Senekal, on October 14, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wani wuri a Afirka Ta Kudu a wannan ranar dai, mutane sun haɗa hannu domin yin addu'a a garin Senekal, inda can ne cibiyar tashin hankali kan hare-haren da ake kai wa Turawa manoma.
UN-recognised Libyan Government of National Accord (GNA) detonate an explosive device, uncovered from areas south of the capital, in the Libyan capital Tripoli on October 12, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Litinin gwamnatin Libiya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yarda da ita ta sanya nakiyar da aka gano a kusa da Tripoli babban birnin ƙasar.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.