Zanga-zangar SARS: Albashin ƴan sandan Najeriya da na wasu ƙasashen duniya

Asalin hoton, Getty Images
A yayin da zanga-zangar da ake yi a Najeriya kan SARS ta shiga mao na uku, daya daga cikin sharudan da masu gangamin ke son gwamnatin kasar ta cka shi ne inganta aikin dan sanda.
Ƴan sandan Najeriya, kamar sauran ƴan sanda a duniya aiki mai matuƙar muhimmanci na kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa.
Irin wannan babban nauyin da ke kan ƴan sanda na tafiya ne da albashi mai tsoka a wasu ƙasashen.
Daga watan Fabrairun 2020, waɗannan jerin ƙasashe ne da suka fi biyan ƴan sanda albashi a duniya, kamar yadda shafin salaryexpert.com ya bayyana.
1. Canada
Canada ce ta fi biyan albashi ga ƴan sanda a duniya inda ɗan sanda ke karbar sama da dala 100,000 a shekara, kwatankwacin naira miliyan 38.
Albashinsu yakan yi tsoka idan aka tura su domin kula da wasu wurare kamar wurin da ake gini ko wani aiki na musamman.
Sannan suna karɓar alawus na lokacin da suka ƙara a wajen aiki.
Sabbin ɗauka a aikin ƴan sanda suna karbar dala 50,000 a shekara, kwatankwacin naira miliyan 19.
2. Switzerland
Ƴan sanda a Zurich, ƙasar Switzerland na karɓar dala 73,472 a shekara, kwatankwacin naira miliyan 28.
3. Amurka
Matsakaicin albashin ɗan sanda a Amurka dala 60,000 kwatankwacin naira miliyan 22, amma wannan ya dogara da jihar da ɗan sanda yake da kuma ƙwarewarsa.
New York da California da New Jersey ne ƴan sanda suka sun fi karɓar albashi mai tsoka
4. Birtaniya
Albashin farko ga ƙaramin ɗan sanda a Ingila da Wales da Arewacin Ireland shi ne tsakanin fam 19,400 (naira miliyan 9.5) zuwa fam 23,000 (naira miliyan 11.2) a shekara.
Amma matsakaicin albashi a Birtaniya shi ne fam 31,000 9naira milyan 15.2) a shekara kuma ba su wuce yin aikin sa'a 40 a mako.
5. Australia
Ƴan sandan Najeriya na karɓar dala dala 42,000 kwatankwacin naira miliyan 16 a shekara a Australia.
Kuma ana biyansu ne kan aiki sa'a 40 a mako kuma idan suka yi aiki fiye da lokacinsu za su samu alawus.

Asalin hoton, Reuters
Nawa ne albashin ƴan sandan Najeriya?
Ƴan sandan Najeriya ne ke karɓar albashi mafi ƙarancin albashi.
Dala 1,700 wato naira 645,842 suke karɓa a shekara kwatankwacin dala $4 a rana.
Ƴawan ƴan sandan Najeriya sun kai 250,000 kuma waɗannan alkalumman na sabbin shiga aikin ƴan sanda ne.











