Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙungiyar Izala: Abin da ya kamata ku sani game da Jami'ar As-Salam da ƙungiyar ke ginawa a Hadejia
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau
- An wallafa
Ƙungiyar addinin Musulunci ta Izalatil Bidi'a Wa Ikamatus Sunnah (JBWIS) ta ce ta kafa Jami'ar As-Salam Global University da zummar "samar da sauƙi ga Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba a arewacin Najeriya".
Shugaban ƙungiyar Sheikh Bala Lau ne ya shaida wa BBC hakan ranar Talata.
A ranar Lahadi ne ƙungiyar ta gudanar da wani taron ƙaddamar da ginin jami'ar a Hadejia da ke jihar Jigawa, inda ya samu wakilcin Shugba Muhammadu Buhari da gwamnoni da 'yan majalisun tarayya da jagororin siyasa.
Mahalarta taron sun bayar da gudummawar kusan naira biliyan ɗaya, wanda Sarkin Musulmi Muhammad Abuabakar Sa'ad III da Ministan Sadarwa na Najeriya Dr. Isa Ali Pantami - wakilin Shugaba Buhari - suka saka ɗambar ginin jami'ar.
A ina mazaunin jami'ar yake?
Jami'ar As-Salam International University na da mazauni na dindindin a garin Hadejia da ke Jihar Jigawa a Arewa Maso Yammacin Najeriya.
"Jami'ar za ta kasance ƙarƙashin kulawar ƙungiyar Izala," in ji Sheikh Bala Lau.
Me ya sa aka kafa jami'ar?
Ƙungiyar Izala ta bayyana dalilai da suka sa ta kafa jami'ar, waɗanda suka haɗa da sauƙaƙa wa 'yan arewacin Najeriya da kuma sauya tunani da ɗabi'ar matasan Musulmi game da ta'addanci.
"Mun kafa jami'ar ne domin sama wa al'ummar Musulmi da ma waɗanda ba Musulmi ba sauƙi na nan arewacin Najeriya kuma mun yi mata suna As-Salam Global University," a cewar Bala Lau.
"Mun yi haka ne musamman saboda yanayin da ake ciki na buƙata, matasammu kusan miliyan biyu na rubuta jarrabawar JAMB duk shekara kuma alƙaluman hukumomin da ke kula da jami'o'i sun nuna cewa ɗalibai 500,000 ne kawai jami'o'inmu ke da ƙarfin ɗauka a duk shekara.
"Kenan ɗalibai kusan miliyan ɗaya da rabi ba sa samun damar shiga jami'a," in ji shi.
Kazalika, Sheikh Lau ya ce suna da niyyar sauya tunani da ɗabi'ar matasan Musulmi "masu amfani da ta'addanci suna tunanin Musulunci ne".
"Hadisin Annabi ya nuna ran Musulmi ɗaya ya fi ɗakin Ka'aba daraja, amma ka duba yadda ake kashe-kashe da sunan addini.
"Bindiga ba ta canza mai aikata wannan ta'addanci tun da tunaninsa na addini ne. Dole sai ya samu ilimi nagartacce ta hanyar jami'a za a samu sauƙin wannan.
"Sannan akwai matasanmu da ke zuwa karatu Sudan ko Masar, kowannensu ya yi karatun addini ko kuma na zamani amma babu inda za su je su yi aiki, ka ga kuwa samar da jami'a ya zame mana lalura."
Ya ƙara da cewa suna fatan ɗaliban da ake yayewa a makarantun sakandare na addinin su ci gaba da karatunsu a jami'ar.
Su wane ne ke ɗaukar nauyin jami'ar?
"Al'umma ne ke ɗaukar nauyin wannan jami'a domin mun ce su bayar da sadakar naira 1,000, 'yan wannan ƙungiya [Izala] da waɗanda ba Musulmi ba sun sanya mana taimako," in ji Bala Lau.
"A irin wannan hali, an samu tallafin naira miliyan 150. Akwai kuma wani ɗan kasuwa a Najeriya da ya ba mu gudunmawar naira miliyan 500. Gwamnoni kusan guda shida sun yi alƙawarin miliyan 50-50.
"Sannan Abdussamad Isiyaka Rabi'u ya ba da miliyan 50 sai kuma ƙaninsa da ya ba mu miliyan 10. Bola Ahmed Tinubu ya ba mu miliyan 10. Sannan akwai waɗanda suka yi mana alƙawarin gina wasu sashe na jami'ar."
Sai dai bai bayyana ƙayyadajjen lokacin kammala ginin jami'ar ba.
Waɗanne darussa za a koyar a jami'ar?
Jami'ar As-Salam za ta koyar da darussan Musulunci da kuma na zamani wato conventional university a Turance, a cewar Malam Bala Lau.
"Baya ga darussan addini, akwai sashen koyar da ilimin boko, har ma muna tunanin buɗe kwalejin aikin likita da injiniyanci da sauran abubuwan da jami'o'i ke yi."
Mece ce alaƙar jami'ar da ƙasashen waje?
Sheikh Bala ya ce "mun kafa wannan jami'a ne a Najeriya kuma dukkan inda muke neman tallafin gudanarwa a Najeriya ne, sannan ba mu da wata buƙatar neman tallafi daga ƙasar waje".
Ya ƙara da cewa suna maraba da duk wanda zai ba su gudummawa domin sun buɗe jami'ar ne domin bayar da tasu gudunmawar "domin ci gaban ilimi a Najeriya".
Mene ne sharuɗan shiga jami'ar?
"Duk wanda ya cika sharuɗan shiga jami'a zai shiga," in ji Bala Lau. "Ta Musulmi ce, ba wai kawai don ƙungiyar Izala ce ta gina sai a ce sai 'yan Izala ne za su shiga ba."
Ya ce kafin a ba su lasisi akwai sharuɗa da aka zayyana musu "saboda haka duk wanda ya cika waɗannan dokokin za a ɗauke shi in Allah Ya yarda".