Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben gwamnan Ondo: Rotimi Akeredolu na jam'iyyar APC ya yi nasara karo na biyu
Hukumar zaɓen Najeriya INEC, ta bayyana Rotimi Akeredolu a matsayin ɗan takarar da ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ondo a ranar Asabar.
Mr Akeredolu ya samu kuri'a 292,830, yayin da dan takarar jam'iyyar PDP, Mr Eyitayo Jegede yake biye masa da kuri'a 195,791, sai kuma dan takarar ZLP, Agboola Ajayi, wanda ya samu kuri'a 69,127.
Dukkanin 'yan takarar uku lauyoyi ne kuma sun fito daga mazaɓun sanata uku daban-daban - Akeredolu daga Ondo ta Arewa; Jegede daga Ondo ta Tsakiya da kuma Ajayi daga Ondo ta Kudu.
Mista Akeredolu ne gwamnan da ke kan mulki a jihar tun shekarar 2016.
Sakamakon ƙananan hukumomin da aka bayyana
Akoko North-West - APC: 15, 809 - PDP: 10,320
Akoko North-East - APC: 16,572 - PDP: 8,380
Akoko South-East - APC: 9,419 - PDP: 4,003
Akoko South-West - APC: 21,232 - PDP: 15,055
Ifedore - PDP: 11,852 - APC:9,350
Akure North - PDP: 12,263 - APC: 9,546
Ile-Oluji/Okeigbo - APC: 13,278 - PDP: 9,231
Akure South - PDP: 47,627 - APC: 17,277
Owo - APC: 35,957 - PDP: 5,311
Idanre - APC: 11,286 - PDP: 7,499
Ondo East - APC: 6,485 - PDP: 4,049
Irele - APC: 12,643 - ZLP: 5,904
OSE - APC: 15122 - PDP: 8421 - ZLP: 1083
OKITIPUPA - APC: 19266 - PDP: 10367 - ZLP: 10120
Ondo West - APC: 15977 - PDP: 10627 - ZLP: 10159
ODIGBO - APC: 23571 - PDP: 9485 - ZLP: 6540
ILAJE - APC: 26657 - PDP: 11128 - ZLP: 4405
ESE ODO - APC: 13383 - PDP: 4680 - ZLP: 4760