Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Singapore za ta biya iyaye kuɗi domin su haifi yara a lokacin annobar korona
Ƙasar Singapore za ta biya 'yan ƙasar kuɗi domin ƙarfafa musu gwiwa don su haifi yara a lokacin annobar korona.
Gwamnatin ƙasar ta damu ne kan cewa 'yan ƙasar sun jingine haihuwa gefe guda inda suka mayar da hankali wurin neman kuɗi da ayyuka.
Har yanzu dai ba a faɗi takamaiman kuɗin da za a biya ba. Singapore na daga cikin ƙasashen duniya da ake samun ƙarancin haihuwar yara, inda ƙasar ta shafe shekaru tana ƙoƙarin ƙara yawan mutanenta.
Sai dai a wani ɓangaren kuma, maƙwabtanta irin su Indonesiya da Philippines na ganin cewa mata da dama na samun ciki a wannan lokaci na annobar korona wanda hakan matsala ce ga ƙasashen.
"Mun samu labarin cewa annobar korona ta jawo wasu iyaye sun fasa shirin da suke yi na haihuwa," in ji mataimakin Firaiminista Heng Swee Keat a ranar Litinin.
Mista Heng ya ce za a fito da bayanai kan adadin kuɗin da za a biya 'yan ƙasar domin ƙarfafa musu gwiwa su haihu.
A halin yanzu dai ana biyan iyayen da suka cancanta garaɓasar kusan dala dubu 10.
Adadin haihuwar da ake samu a ƙasar ya ragu na shekara takwas a jere a 2018, kamar yadda wata ƙididdiga da gwamnatin ƙasar ta fitar ta nuna.
Akwai ƙasashe da dama a yankin Asiya waɗanda ke fuskantar matsaloli irin na rashin haihuwa, inda ake ganin lamarin zai ƙara ta'azzara a wannan lokaci na korona.
"A farkon wannan shekara, an samu raguwa matuƙa a yawan haihuwar da ake yi a ƙasar China, ba a taɓa samun irin wannan raguwar ba tun bayan kafuwar jam'iyyar People's Republic of China shekara 70 da suka wuce.
Samun ƙaruwar haihuwa
Wasu daga cikin ƙasashen da ke makwabtaka da Singapore su kuma yawan haihuwar ce ta dame su.
A ƙasar Philippines, an yi hasashen cewa za a haifi yara kusan miliyan 2.6 idan aka ci gaba da saka takunkumin korona, kamar yadda Asusun ƙidaya na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana a ƙasar.
"Wannan adadin wata annoba ce ita kanta," in ji Aimee Santos, wani mai magana da yawun MDD a Philippines a watan da ya gabata.
Philippines ita ce ƙasa da ta fi kowace yawan jama'a a Kudancin Asiya inda take da mutum 108.4. Ƙasar ce take da adadi mafi yawa na annobar korona a yankin inda mutum 307,0000 suka kamu.