Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mali : Shugaban riko na Mali ya kafa majalisar zartarwa
Shugaban rikon kwarya na Mali, Bah Ndaw, ya kafa majalisar zartarwa mai mambobi ashirin da biyar inda aka ba wa manyan jami'an soji mukamai da dama.
A cewar wata dokar shugaban kasar da aka karanta kai tsaye ta gidan talabijin din kasar, ma'aikatar tsaro, da ma'aikatarr gudanar da al'amuran cikin gida da ta sasanci za su kasance karkashin jagorancin wasu manyan hafsoshin sojan kasar ta Mali.
Bah Ndaw - wanda ke da kwarewa a aikin sojan sama, ya zabi madugun juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin shugaba Boubakar Keita a matsayin mataimakinsa.
Bayan nada farar hula a matsayin Firai minista, kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS na sa ran janye takunkuman da ta kakabawa kasar sakamakon juyin mulkin na watam Agusta nan ba da jimawa ba.
Wanene Bah Ndaw ?
An haifi tsohon sojan a ranar 23 ga watan Agustan 1950 a yankin Segou.
Yana da shaidar karatu a fanin soji daga Faransa da wata shaidar makarantar yaki ta CID a 1994. Yana da kwarewa sosai a fanin sojin sama.
Tsohon ministan tsaro da harkokin cikin gida ya fito ne daga rukuni na 7 na 1973 daga makarantar dakarun hadin-gwiwa (EMIA), da ke Koulikoro.
Bayan ya kammala karatu ya shiga soji a matsayin mai bada taimakon sa kai a ranar 1 ga watan Yunin, 1973.
Da shekara ta zagayo sai aka zabe shi domin yin kwas kan tuka helikwafta ga tsohuwar Rasha.
A ranar 27 ga watan Maris din 2014, tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya nada shi Ministan harkokin tsaro da tsoffin sojoji.
Kanar-Manjo Bah N'Daw, da abokansa ke kira "the great" saboda tsayinsa (1.95 m), tsohon matukin helikwafta ne kuma ya taba zama mataimaki ga Janar Moussa Traoré.
Daga 2008 zuwa lokacin ritayarsa a 2012, Kanar-Manjo Bah N'Daou shi ne daraktan tsoffin sojoji na kasa da wadanda yaki ya shafa.
Manjo Janar Bah N'Daw jami'in sojin kasa ne daya sha karbar manyan kyaututtuka na soji da na ƙasa.
Ana dai bayyana shi a matsayin mai jajircewa da hazaka a fanin aikin soja.