Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coronavirus: Shin cutar ta wuce ganiyarta a Afrika?
- Marubuci, Daga Peter Mwai da Christopher Giles
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check
- An wallafa
Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO, ta bayyana cewa annobar korona a nahiyar Afrika ta wuce ganiyarta, amma ta yi gargaɗin cewa kada ƙasashe su shantake a daidai lokacin da suke sassauta dokokin korona.
Adadin mutanen da ake samu suna kamuwa da cutar a kullum na raguwa matuƙa, kusan watanni biyu kenan, duk da cewa ana samun ƙaruwar cutar a wasu ƙasashen.
Ya saurin bazuwar korona yake?
Kusan makonni hudu da suka wuce kenan, an samu raguwa da kusan kashi 1.7 cikin 100 a adadin mutanen da ake bayar da rahoton cewa sun kamu da cutar a kullum, kamar yadda cibiyar da ke yaƙi da yaɗuwar cutuka ta Afrika wato CDC ta bayyana.
Sai dai CDC ɗin ta bayyana cewa ba a gama tsira ba.
"Ba na tunanin an kawo ƙarshen ɓullar annobar, ba mu kai ƙasa ba har yanzu," in ji John Nkengasong daga hukumar CDC.
Akwai kuma wasu ƙasashe da ake samun ƙaruwar masu kamuwa da cutar.
Yankin Arewacin Afrika ya samu ƙaruwa da kusan kashi 14 cikin 100 na masu kamuwa da cutar a makonni huɗu da suka gabata, wanda shi ne yanki ɗaya tilo da ke bayar da rahoto kan ƙaruwar masu kamuwa da cutar.
Ƙaruwar masu kamuwa da cutar ya faru ne sakamakon mutanen da ake samu suna kamuwa da cutar a ƙasashen Morocco da Tunisia da Libiya.
Morocco na samun ƙaruwar sabbin mutane da ke kamuwa da cutar, kuma an ga yadda mutane da dama suka kamu da korona a ƙasar cikin makonni huɗu da suka gabata.
Tunisia da Libiya na daga cikin ƙasashen da suke da adadi mafi yawa na masu kamuwa da cutar a makon da ya gabata.
Sauran ƙasashen da ke bayar da rahoto kan sabbin masu kamuwa da cutar su ne Afrika Ta Kudu da Ethiopia.
Sai dai wata ƙungiyar bayar da agaji ta global humanitarian relief body ta bayyana cewa tana ganin cewa mutanen da ke da cutar ta korona a nahiyar Afrika sun wuce haka.
Ta ce ƙarancin gwajin da ake yi ne ya sa ba a samun adadi mai yawa.
Ita ma WHO ta bayyana cewa sauyi da aka samu na adadin waɗanda ake yi wa gwaji ya sa ba a samun adadi mai yawa.
Misali ɗaya shi ne ƙasar Kenya, inda adadin waɗanda ke kamuwa da cutar ke ta raguwa sama da wata ɗaya kenan, bayan ƙasar ta sauya yadda ta ke gwaji inda ta ke yi wa mutanen da suke da suke cikin haɗari ƙwarai gwajin
Wasu ƙasashen kuma kamar Ethiopia, sun ƙara adadin waɗanda suke yi wa gwaji a kullum. Ana samun ƙaruwar cutar a ƙasar tun tsakiyar watan Yuni, amma a yanzu ana samun raguwar masu kamuwa da cutar.
Waɗanne ƙasashe ne cutar ta fi yi wa illa?
Afrika Ta Kudu ita ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa a Afrika yawan masu korona da kuma waɗanda suka mutu, kuma ita ce ƙasa ta 10 a duniya a yawan masu cutar.
Ana samun raguwar mutanen da ke kamuwa da kuma waɗanda ake kai wa asibiti a ƙasar kusan watanni biyu kenan.
Ministan lafiya na ƙasar, Zwelini Mkhize, ya bayyana cewa a hukumance dai ƙasar ta samu sauƙin cutar.
Sai dai kuma akwai damuwa kan cewa akwai waɗanda ke da cutar waɗanda ƙasar ba ta san da zamansu ba.
Bincike daga cibiyar bincike ta likitoci a ƙasar ya bayyana cewa akwai yiwuwar adadin waɗanda suka mutu sakamakon cutar ya wuce yadda aka faɗa.
Ta bayyana cewa ƙaruwar mace-mace kan yadda aka saba samu a baya ya ƙaru da kusan 17,000 - wannan na nufin da kusan kashi 59 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar bara.
A halin yanzu, Morocco ta wuce Masar kuma ita ce ta biyu biyu a yawan waɗanda suka kamu da cutar amma duk da haka Masar ce ta biyu a yawan waɗanda cutar ta kashe a nahiyar Afrika.
Masar ce ta uku a yawan waɗanda suka kamu da cutar ta korona, sai kuma Ethiopia da kuma Najeriya.