Za a kashe malamar da ta sanya wa ɗalibanta guba a cikin kunu a China

An wallafa

Wata kotu a kasar China ta yanke wa wata malamar makarantar kananan yara hukuncin kisa a bisa zargin sanya wa dalibanta 25 guba, inda daya daga cikinsu ya rasa ransa.

A shekarar da ta gabata ne aka cafke Wang Yun bayan da aka garzaya da kananan yaran dalibai a birnin Jiaozuo zuwa asibiti baya sun shan kununsu na safe.

Kotun ta ce malamar da zuba sinadarin sodium nitrite ne a cikin abincin karin kumallon ɗaliban abokiyar aikinta, don ɗaukar fansa bayan wata sa-in-sa da ta shiga tsakaninsu.

Kotun da bayyana Ms Wang a matsayin "mara imani kuma mamugunciya".

Lamarin wanda ya faru a ranar 27 ga watan Mayun shekarar bara ya girgiza kasar ta China tare da jan hankulan kafafen yada labaran kasashen waje.

A ranar Litinin ne wata kotu a yankin da ke birnin Jiaozuo ta yanke wa Ms Wang din hukuncin kisan.

Ta kuma bayyana a wata sanarwa cewa ta watsa sinadarin sodium nitrite a cikin kunun kananan daliban wata malamar a matsayin ''ramako'', bayan da suka yi wata ''sa-in-sa kan harkokoin tafiyar da dalibai''.

Ana dai yawan amfani da sinadarin na sodium nitrite wajen adana ɗanyen nama don ka da ya lalace, amma kuma ya kan zama hadari idan aka yi amfani da shi fiye da ƙima.

Kotun ta kuma ce wannan ba shi ne karon farko da Ms Wang ta taɓa saka wa mutane guba a abinci ba, in da ta yi misali da lokacin da matar ta sayi sinadarin na nitrate a shagon kafar sadarwa ta internet inda ta saka wa mijinta cikin abincin da ya yi masa lahani.

A cikin watan Janairun wannan shekarar ne da ya daga cikin yaran da ta saka wa gubar ya rasu ne a asibiti ya rasu bayan shafe watanni goma yana jinya a asibiti.

Kotun ta kara jaddada cewa Ms Wang "maras imani ce kuma muguwa, kan mummunan laifin da ta aikata mai girma ne da ya cancanci hukunci mai tsanani.''

Yayin da kasar China ta ƙi amincewa ta bayyana yawan adadin mutanen da ta yankewa hukuncin kisa, kungiyoyin kare hakkin bil adama sun yi amanna cewa kasar na kashe dubban mutane a ko wace shekara.

Ana amfani da allurar guba ko kuma bindigewa wajen yanke hukuncin kisan.