Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fafaroma Francis: Babban mai ba da shawara ga shugaban ɗarikar Katoli ya ajiye muƙaminsa
Babu zato babu tsammani, mai bai wa Fafaroma Francis shawara ya ajiye mukaminsa.
Giovanni Angelo Becciu na daga cikin tsiraru da ke da mukamin Cardinal a fadar Vatican.
A baya ya taɓa aiki a matsayin mutun na biyu mafi girma a sakatariyar Vatican.
Sunan Mr Becciu ya fita a badaƙalar sayen gidajen alfarma a birnin London da kudin asusun coci da nufin siya mata kadarori, wanda har yanzu a na kan bincike.
To amma tsohon Cardinal din ya musanta zargin aikata ba dai dai ba.
Sanarwar da Holy See ta fitar na cewa ''Fafaroma Francis ya aminta da murabus da kuma ajiye mukamin Cardinal da mai girma Giovanni Angelo Becciu ya yi''.
To sai dai ba ya ga sanarwar ajiye mukamin, fadar Vatican ba ta ba da wani karin bayani ba.
A bara an kori ma'aikatan fadar su biyar, bayan wani samame a sakatariyar, a lokacin da ƴan sanda su ka kwashi kwamfyutoci da kuma wasu muhimman takardu.
Mr Becciu ya zama Cardinal a shekarar 2018, kuma zai cigaba da rike mukamin duk da murabus din da yayi.
To amma ba zai samu tikitin zaɓar sabon Fafaroma ba a nan gaba.
A baya Cardinal O'Brien ya rasa damar sa ta zaɓar sabon Fafaroma, bayan da ya yi murabus a shekarar 2013 bisa zargin aikata lalata