India: Mutumin da ya 'farka cikin matarsa don sanin abin da za ta haifa'

An wallafa

'Yan sanda a Indiya sun ce matar da ake zargin mijinta ya yanka cikinta ta haifi jarirn babu rai.

Iyalan matar sun yi zargin cewa mutumin ya yanka cikin matarsa domin sanin jinsin jaririn da za ta haifa.

Sun ce ma'auratan biyu suna da 'ya'ya mata biyar kuma mijin ya daɗe yana matsa mata domin ta haifi namiji.

Mutumin, wanda aka kama, ya ce ba da gangan ya ji wa matarsa rauni ba, yana mai cewa ya yi hakan ne bisa kuskure.

Lamarin ya faru ne a yankin Badaun a Uttar Pradesh, jiha mafi yawan jama'a a arewacin Indiya.

Jami'an ƴan sanda sun shaida wa BBC cewa yanzu matar tana kwance a asibiti inda take samun sauƙi a Delhi, babban birnin ƙasar, kuma tuni aka tsare mijin nata.

'Yar uwar matar ta shaida wa manema labarai a kasar cewa ma'auratan biyu sun daɗe suna kai ruwa rana kan neman ɗa namiji.

A cewar ɗan uwan matar, an kai 'yar uwar tasa wani asibiti a Delhi ranar Lahadi sakamakon shawarar da likitoci suka bayar saboda tsananin da jikinta ya yi.

Mutumin ya ce ba da gangan ya yanka cikin matarsa ba. Ya shaida wa manema labarai cewa ya jefa mata lauje, amma bai yi zaton zai raunanata sosai ba.

"Ina da 'ya'ya mata biyar, ɗana namiji ya mutu. Na san cewa 'ya'ya kyauta ce daga Allah. Yanzu duk abi nda ya faru na fawwalawa Ubangiji."

'Yan sanda suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Bukatar iyaye a India ta haifar 'ya'ya maza maimakon mata ta haifar da rashin daidaito kan jinsin 'yan kasar.

'Yan mata kusan miliyan 46 ne suka ɓata a India a shekara 50 da suka gabata, a cewar wani rahoto na hukumar majalisar dinkin duniya da ke kula da yawan al'umma a duniya.

A duk shekara, ana kashe a ƙalla mata 460,000 ta hanyar zubar da ciki saboda ba a son haifarsu.

A 2018 wani rahoto na gwamnatin India ya ce son haifar 'ya'ya maza ya haifar da mata miliyan 21 da "ba a bukatarsu". Wani rahoton ma'aikatar kudin kasar ya ce ma'aurata suna hayayyafa sosai har sai sun haifi 'ya'ya maza.