Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An sake bude Taj Mahal bayan dokar kullen korona
Shahararren wurin tarihin nan na Taj Mahal zai sake buɗe ƙofofinsa ga ɗumbin masu ziyara bayan wata shida - lokaci mafi tsawo da aka taɓa ɗauka wajen na garƙame.
An rufe wurin ne yayin da ƙasar ta saka dokar kulle a watan Maris domin hana bazuwar annobar korona.
A yanzu za a bar mutum 5,000 su kai ziyara wajen kowace rana tare da tabbatar da bin matakan kariya ga korona yayin da ake samun ƙaruwar masu cutar a Indiya.
Taj Mahal ɗaya ne daga cikin manyan wuraren buɗe ido da mutum 70,000 ke zuwa duk rana kafin zuwan annobar.
Sarki Shah Jahan ne ya gina Taj Mahal a ƙarni na 17 domin tunawa da sarauniya Mumtaz Mahal.
A shekarar 1978 ma an taɓa rufe wajen lokacin da birnin Agra inda ginin yake ya fuskanci matsalar ambaliyar ruwa. Sannan kafin nan an rufe wajen na 'yan kwanaki a shekarar 1971 lokacin wani yaƙi tsakanin India da Pakistan.
An ba da izinin ɗaukan hoton selfie amma ban da wanda mutane da dama za su ɗauka
An tsaftace wajen kafin buɗe ƙofofi da ƙarfe 8 na safe sannan duk jami'an an hange su sanye da takunkumi, kamar yadda ɗan jarida Yogesh Kumar Singh wanda ya ziyarxi wajen lokacin da aka buɗe ya shaida wa BBC.
Hukumomi sun ce za a riƙa yin gwajin zafin jiki a ƙofar shiga wurin sannan za a buƙaci masu ziyara su yi amfani da intanet wajen sayen tikiti.,
An kuma faɗa musu su riƙa bin shawarar ba da tazara.
Yayin da masu ziyara suke da damar ɗaukan hoton Selfie, an hana yin hoton mutane da dama.
"Amma babu cunkoso, kamar ba Taj Mahal ba," in ji Mr Singh. "Ina tunanin mutane da dama ba za su ziyarci wajen ba idan ana ci gaba da samun ƙaruwar masu korona."
India ta ba da rahoton sama da mutum miliyan biyar da suka kamu da cutar a ƙasar kuma Uttar Pradesh, inda Taj yake, shi ne yanki na biyar da aka fi samun yawan masu cutar.
Mr Kumar ya ce zai zama wani abin burgewa a ga yadda hukumomi za su tabbatar da matakan kariya idan mutane da dama suka fara kai ziyara wajen.
Taj dai a zagaye yake da gandu inda masu ziyara ke zama domin ɗaukar hotuna. Amma rufaffen waje ne da kusan babu gudanar iska lamarin da zai sa a yi saurin yaɗa korona.
Wajen cike yake da mutane yayin da masu ziyara ke shige da fice a wajen.
Babu cukowa a Taj
Gautam Sharma, wanda ya taho daga Delhi domin kai ziyara Taj Mahal ranar Litinin ya ce ya shafe tsawon watanni yana jiran wannan rana ta zo.
"Na san ba duk mutane ne za su zo ba, shi ya sa na yi tunanin dama ce gare ni na ziyarci wajen cikin ranakun farko da sake buɗe shi," a cewarsa.
Sai dai ba a samu cukowar mutane ba yayin da aka buɗe wajen da safiyar Litinin - wani abu da ba kasafai ake gani ba a tarihin wajen.
Wannan ne wuri mafi shahara a India. Shugaban Amurka Donald Trump da mai ɗakinsa Melania zun ziyarci Taj a watan Fabrairu.
Sauran shugabannin duniya da suka ziyarci wajen sun haɗa da Firaministan Canada Justin Trudeau da Shugaban Rasha Vladimir Putin.