Kalli gyararre da nannaɗaɗɗen gashi cikin hotunan Afrika na mako nan: 11 - 17 ga Satumban 2020

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotuna daga nahiyar Afrika da kuma na wasu ƴan Afrika a sassan duniya:

Canoeists paddle together in the twilight.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wasu mutum uku sun shiga kwale-kwale a madatsar ruwan Emmarencia a Johannesburg da sassafe ranar Talata, a Afrika Ta Kudu.
A hairdresser slicks a customer's edges with his fingertips.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kwanaki kaɗan bayan hakan a kusa da wannan wajen wato Soweto, wata mata ta je shagon gyaran kai...
A client leaves a salon after having her hair done.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ga ta nan ta fito daga wajen gyaran gashin a ranar Juma'a bayan an gyara tare da nannaɗe gashin.
Three women are seen jumping and landing in a 3000m steeplechase event.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadi kuma Hyvin Kiyeng da Mercy Chepkurui da kuma Beatrice Chepkoech - dukkansu ƴan Kenya - a wajen gasar tsalle-tsalle a Jamus.
Schoolchildren in uniform stand in a queue.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata ɗaliba da ke jin barci tana hamma a ranar Talata ranar da aka buɗe makarantu a Tunusiya a karon farko tun dokar kullen annobar cutar korona a watan Maris.
Henri Konan Bédié stands on a podium waving at crowds in Yammousoukro.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Asabar dubban magoya baya suka halarci wani gangami a baban birnin Ivory Coast tare da Henri Konan Bédié, wanda zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen da za a yi a watan gobe. Babban abokin adawarsa na tsawon lokaci Alassane Ouattara wanda ke neman takarar a karo na uku sakamakon mutuwar bazata ta ubangidansa na siyasa Amadou Gon Coulibaly.
A picture of flooded land taken from aboard a Bahrain Royal Charity Organisation (RCO) aircraft.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Litinin aka ɗauki hoton illar da mummunar ambaliyar ruwa ta yi ga babban birnin Sudan wato Khatoum.
Ecowas and CNSP representatives sit at table surrounded by flags and other emblems of state in Accra, Ghana.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Shugabannin ƙungiyar Ecowas suna tattauna wa da sojojin Mali a ranar Talata, kan batun miƙa mulki ga farar hula sakamon juyin mulkin watan da ya gabata.
Children and adults wait on a pavement next to an illusatration of George Bizos.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Anan kuwa ƴan Afrika Ta Kudu ne suke jira su miƙa girmamawarsu a wajen jana'izar George Bizos, wanda ya yi fafutukar adawa da nuna wariyar launin fata. Lauyan mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, wanda ya wakilci Nelson Mandela a wajen shari'ar Rivonia ya mutu ne a makon da ya gabata yana da shekara 92.

Haƙƙin mallakar hotuna na Reuters da EPA da AFP ne.