Zanga-zanga a Benghazi: Gwamnatin Khalifa Haftar ta yi murabus

An wallafa

Gwamnatin Libiya mai shalkwata a birnin Benghazi ta sanar da yin murabus bayan mummunar zanga-zanag kan kan tsadar rayuwa da rashawa.

A zanga-zangar baya-bayannan, an cinnawa ofishin ginin shalkwatar gwamnati karkashen Khalifa Haftara wuta birnin Benghazi.

Tashin hankalin da ya barke tun daren Asabar a al-Bayda, inda gwamnati ke da ofishinta, da Sabha a kudancin kasar, da kuma al-Marj a karon farko wanda wuri ne da Janar Haftar ke iko da shi.

Wani mai magana da yawun Janar Haftar yace gwamnatinsa na goyon bayan zanga-zangar lumana, amma ba za ta bar 'yan ta'adda da Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi su kankane fafutukar ba.

A baya dai, an fi gudanar da zanga-zanga ne a babban birnin kasar Tarabulus, inda gwamnatin da Majalisar Dinkin Dunuiya ke goyawa baya take.

Libya ta dare gida biyu tun 2014. Gabashin Libya da yawancin kudancin kasar na karkashin dakarun Janar Haftar.

Wani yunkuri da dakarun nasa suka yi tsawon wata 14 domin kwace babban birnin kasar Trabulus ya ci tura.

A Tarbulus ne gwamnatin da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya ke da shakwatarta kuma yawancin kasashen yammacin duniya ita suke mara wa baya.