Kyawawan hotunan Afirka na makon 4-10 ga Satumban 2020

An wallafa

Zababbun hotunan Afirka da 'yan Afirka a wasu nahiyoyin na wannan makon.

Members of the Tigray Circus rehearse in the city of Mekele, Ethiopia, on September 8, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Talata, mambobin Tigray ta masu wasan lanƙwasa suna atisaye a birnin Mekeele da ke kasar Habasha…...
Members of the Tigray Circus rehearse in the city of Mekele, Ethiopia, on September 8, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ... kungiyar tana bayar da horo ga matasa marasa galihu.
A ranar Juma'a, wani tsohon dan wasan kokawa na kasar Congo Maitre Satonge ya halarci jana'izar tsohon abokin aikinsa kuma abokinsa, Alphonse Mwimba Makieasa, wanda aka fi sani da fafutukar kare hakkokin zabaya da ya mutu bayan ya shafe shekara daya yana jinya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Juma'a, wani tsohon dan wasan kokawa na kasar Congo Maitre Satonge ya halarci jana'izar tsohon abokin aikinsa kuma abokinsa, Alphonse Mwimba Makieasa, wanda aka fi sani da fafutukar kare hakkokin zabaya da ya mutu bayan ya shafe shekara daya yana jinya.
Masu fafutuka daga jam'iyyar adawar Afirika ta Kudu, Economic Freedom Fighters sun yi zanga-zanga a wajen shagon Clicks a Polokwane ranar Litinin a kan wani tallan kayan wanke gashi da ya nuna bakin gashi a matsayin mara kyau sannan gashin turawa a matsayin abu mai kyau.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu fafutuka daga jam'iyyar adawar Afirika ta Kudu, Economic Freedom Fighters sun yi zanga-zanga a wajen shagon Clicks a Polokwane ranar Litinin a kan wani tallan kayan wanke gashi da ya nuna bakin gashi a matsayin mara kyau sannan gashin turawa a matsayin abu mai kyau.
A ranar Laraba an mayar da wata makaranta a matsayin wurin yin zabe na 'yan majalisar yankin Tigray a Arewacin Habasha.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Laraba an mayar da wata makaranta a matsayin cibiyar zabe na 'yan majalisar yankin Tigray a Arewacin Habasha...
Man walks out of polling station

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ...Gwamnatin Firaiministar Habasha Abiya Ahmed ta ɗage dukkanin zabe saboda annobar cutar korona sannan ta bayyana zaben da aka yi a matsayin haramtacce...
Zaben ya fito da babban kalubale ga ikon da Mr Abiy yake da shi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ... zaben ya fito da babban kalubale ga ikon da Mr Abiy yake da shi.
A ranar Talata mutane a babban birnin Sudan, Khartoum suna ci gaba da fama da ambaliyar ruwa…

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Talata mutane a babban birnin Sudan, Khartoum suna ci gaba da fama da ambaliyar ruwa…
A fadin kasar, ambaliyar ruwa ta kashe kusan mutane dari sannan ta sa dubbai sun rasa gidajensu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ... a fadin kasar, ambaliyar ruwa ta kashe kusan mutane dari sannan ta raba dubbai daga gidajensu.
Haka lamarin yake a Dakar babban birnin Senegal, inda ambaliyar ruwa ta yi barna sosai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Haka lamarin yake a Dakar babban birnin Senegal, inda ambaliyar ruwa ta yi barna sosai.
A ranar Litinin aka dauki wannan hoton a unguwar Kibera da ke Nairobi, a babban birnin Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Litinin aka dauki wannan hoton a unguwar Kibera da ke Nairobi, a babban birnin Kenya
A ranar Talata, masu zanga-zanga a London sun bukaci a biya wadanda malalar mai a yankin Naijar Delta da ke Najeriya ta shafa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Talata, masu zanga-zanga a London sun bukaci a biya wadanda malalar mai a yankin Naijar Delta da ke Najeriya ta shafa.

Hotuna daga AFP, Getty Images, EPA da Reuters.