Wutar dajin Amazon: Shin ta fi muni a bana fiye da baya?

An area of the Amazon burning

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Jack Goodman and Christopher Giles
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Reality Check and Visual Journalism
  • An wallafa

Kare dajin Amazon na da matukar muhimmanci a duniya a yakin da ake da matsalar sauyin yanayi, amma yana fuskantar barazanar gobarar daji, inda galibi yake shafe filayen noma.

Adadin a farkon shekara ya nuna cewa wutar na karuwa, wanda ke cusa damuwa ga masana kimiyya.

A kwanan baya Shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya yi ikirarin cewa "ci da wuta" da dajin Amazon yake yi ba gaskiya ba ne, duk da alkalumman da gwamnatinsa ta wallafa da ke nuna yadda wutar ke bazuwa.

To me alkalumma suka nuna game da abin da ke faruwa a bana?

Shin dajin a Brazil yana ci da wuta?

Brazil babbar kasa ce da ke da yanayin kasa daban-daban, da suka kunshi ƙasa mai ciyayi da dausayi da kuma dazuka.

Brazil ke da kusan kashi 60 na dajin Amazon, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen karbar gurbataccen iska na CO2 mai cutarwa wanda zai iya bin sararin samaniya. Don haka akwai damuwa da ake nunawa musamman game da barnar da wutar za ta haifar.

Adadin yawan wutar dajin Amazon na Brazil kafin watan Yuli ta ƙaru - amma ta ɗan ragu kamar lokacin a bara.

Amma akwai damuwa kan yadda wutar ke ruruwa a watan da ya gabata, fiye da yadda aka yi tsammani.

"Idan muka yi la'akari da matsakaicin adadi a watan Yuli, tsakanin 2010 zuwa 2019, kenan yawan wutar a Yulin 2020 ya ƙaru da kashi 55.6 ckin 100," in ji Farfesa Marcia Casto, masaniyar kimiya 'ƴar Brazil a jami'ar Harvard.

An samu ƙaruwar a watan Yuni (Da kashi 19.6 cikin 100 idan aka kwatanta da Yunin bara, kuma kashi 36.1 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Yuni tsakanin 2010 zuwa 2019). An ga girman gobarar a bana tsakanin Agusta zuwa Satumba.

"Yanayin ƙaruwar wutar a Yuni da Yuli abin damuwa ne," inji Farfesa Castro.

Sunset in the Amazon region

Asalin hoton, Getty Images

Kuma girman a Agusta ya nuna zai yi daidai da wanda aka gani a bara. Wutar a bana ita ce ta biyu mafi girma tun 2010.

A watanni bakwai na farkon 2020, sama da girman daji 13,000sq km na dajin Amazon ya ƙone, kamar yadda bayanan binciken tauraron ɗan adam ya nuna daga Dakta Michelle Kalamandeen, masaniyar dajin Amazon.

Wannan ya ninka girman Landan sau takwas.

Dakta Kalamandeen ta ce dajin da ya ƙone za a ɗauki lokaci kafin ya dawo daidai yadda yake.

"Idan an rasa daji, ya tafi kenan. Zai iya farfaɗowa amma ba ɗari bisa ɗari ba," inji ta.

Idan ka dubi yadda wutar ke bazuwa a Brazil, lokacin mako na 11 na Agusta, akwai alamun wutar dajin a Amazon, yayin da Para da Mato da Grosso da Amazonia da Rondonia ke bayar da rahoton ruruwarta.

Map

A yankunan Novo Progresso a jihar Para, manoma sun yi jimami na kwana ɗaya a bara kuma tauraron ɗan adam ya nuna sama da 1,300 da wutar ta kama a watannin baya, kamar yadda bayanan hukumomi suka tabbatar.

Zuwa arewa maso gabashi, yankin Altamira da dama ne wutar ta laƙume a dajin Amazon na Brazil a wannan lokacin.

An aerial shot from 2019 of deforestation in the Amazon

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani yankin da aka yi saran itace a dajin

Me zai sa ta yi muni a bana?

Masanin kimiyyar yanayi na Brazil Carlos Nobre ya ce akwai abu biyu da ke haifar da gobarar a bana.

Na farko shi ne yadda wannan lokacin rani a bana ya bushe fiye da yadda aka saba.

"Ruwan Atlantic sun fi ɗumi a bana idan kuma haka ta faru, za a samu ƙarancin ruwan sama a kudancin Amazon," inji Farfesa Nobre.

Na biyu kuma shi ne akwai dazukan da aka sare a bara da suka rage - itacen da aka sara na iya ƙara ruruwar wutar.

Boy on horse in Para state, Brazil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An samu bayanan faruwar wutar daji a sassan Brazil

Yawanci ba su ƙone ba domin akwai fafutika ta soji da ke yaki da saran daji.

A bana, sojoji sun kaddamar da samame domin hana saran itace tun watan Yuni da Yuli, shugaba Bolsonaro ya kafa dokar wata hudu ta hana saran daji.

Ba a dade ba mataimakin shugaban kasa Hamilton Mourao ya kaddamar da wani kamfen na yaki da wutar daji, da ya kunshi samar da wata manhaja da mutane za su dinga bayar da rahotanni.

"Za mu fita a Agusta domin hana wannan wutar da ta zarta ta bara," kamar yadda ya shaida wa BBC.

Masu fafutika da ƴan adawar gwamnati na ci gaba da kasancewa a cikin shakku, inji Camilla Costa, wakiliyar BBC.

A cewar ma'aikatar tsaron Brazil, an kwace itace masu yawa da suka kai mita 28,100 da kuma tara da ta kai miliyan 407.2 na kudin Brazil, kwatankwacin dala miliyan 72.6

Amma, wutar ta na ci gaba da bazuwa kuma masu suka na koke kan rashin daukar mataki.

Shin daji na ci da wuta a wasu ƙasashen?

Yawan wutar da ke ci a dajin Amazon a yankin Colombia da Peru da Venezuela ya karu a wannan lokacin fiye da bara.

Ga ƙasashen Amazon, haƙo ma'adinai na ƙara haifar da saran itace wanda kuma ke haddasa wuta, a cewar Dr Kalamandeen.

A Venezuela, an samu karuwar aikin haƙo zinari wanda kuma ake ganin ya kara ruruwar wutar yayin da tun 2016Sshugaba Nicolas Maduro ya buɗe bangaren domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar da ya taɓarɓare

A colombia, bayan sasantawar gwamnati da ƴan tawayen Farc a shekarun da suka gabata, manoma sun koma noma a yankin, wanda ya kara haifar da ruruwar wutar inji Dr Kalamandeen.

Reality Check branding