Darul-Salam a Najeriya: Abubuwa 5 da ba ku sani ba game da ƙungiyar

Asalin hoton, Getty Images
Masana harkokin tsaro sun ce bayyanar wata ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya mai aƙidu irin na Boko Haram babbar barazana ce ga Najeriya da ke fama da hare-haren ta'addanci a sassan ƙasar.
A ranar Laraba ne rundunar sojin kasar ta ce dakarunta sun tarwatsa wani sansanin wata ƙungiya da ake kira Darul-salam (Darul Islam) a yankin Uttu da ke ƙaramar hukumar Toto a jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya.
Sojojin na Najeriya sun ce suna tsare da mambobin ƙungiyar fiye da 400 da suka suka ce sun miƙa wuya gare su - yawancin su mata da yara ƙanana.
Rundunar sojin ta ce ta gano wata cibiya da ƙungiyar ta ke ƙera abubuwan fashewa da rokoki da gurneti kamar yadda Kwamanda Abdussalam Sani, kakakin cibiyar samar da bayanai a kan arangamar da sojojin Najeriya ke yi sassan Najeriya, ya shaida wa BBC.
Sai dai ya ce shugabannin ƙungiyar ba su cikin waɗanda suka miƙa wuya.
Mazauna yankin Uttu a jihar Nasarawa sun ce ƙungiyar Darussalam ta daɗe mayaƙanta na kai musu hari, kuma sun halaka mutane da dama da kuma ƙona garuruwan da ke yankin, ciki har da garin Dausu.
Hakimin Dausu Alhaji Idrisu Mundi Yakubu ya shaida wa BBC cewa ƙungiyar ta tilasta wa jama`arsu da dama yin gudun hijira.
Yaushe Darul-salam ta bayyana?
A watan mayun 2020 ne gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana wanzuwar ƴan kungiyar Darul-salam a jihar.
Gwamnatin Nasarawa ta ce ƙungiyar ta addabi al`ummar karamar hukumar Toto da hare-hare.
Ba a dade ba da sojojin Najeriya suka ce dakarunsu sun gwabza da maharan. Sai dai zuwa yanzu ba a kai ga fayyace babbar manufarsu ba.
Amma masanin tsaro kuma mai bincike kan ayyukan Boko Haram, Barista Bulama Bukarti, ya shaida wa BBC cewa Darul-salam ta riga Boko Haram ɓulla, amma ba ta zafafa ayyukanta ba kamar Boko Haram.
"Su Darul-salam ba su tilasta wa mutane shiga aƙidarsu, saɓanin Boko Haram da ke tursasawa mutane," in ji shi.

Mece ce aƙidar Darul-salam?

Asalin hoton, Getty Images
Kamar Boko Haram, Darul-salam ma ƙungiya ce mai wata aƙida ta musulunci a arewacin Najeriya.
Bulama Bukarti ya ce Darul-salam mutane ne masu aƙida da suka yi imanin cewa Najeriya tana cike da dattin laifufuka da rashin bin Allah da wasu abubuwan da ba su dace ba.
Darul-salam da Boko Haram dukkaninsu sun yarda cewa yan Najeriya kafirai ne muddun ba su yi hijira ba sun koma inda suke.
"Akidarsu ba za ka zama musulmi ba sai ka ƙaura daga birane na Najeriya zuwa daji ka zauna tare da su."
Amma Barista Bukarti ya ce bambancinsu da Boko Haram shi ne ƴan Darul-salam ba su kashe mutane ko jami'an tsaro. "Asalinsu ba su yin kisa kamar yadda Boko Haram suke yi," a cewarsa.
"Darul-salam aƙidarsu suna cewa zuhudu suke yi wato kamar gudun duniya suke yi, shi ya sa suka bar garuruwa suka koma daji da zama. Kuma ba ya cikin aƙidarsu cewa dole sai sun tilasta wa wani mutum shiga ƙungiyarsu."
Alaƙar Darul-salam da Boko Haram
Ƴan Boko Haram da Darul-salam sun taba neman yin ƙawance da juna ganin yadda kusan aƙidarsu ke tafiya daidai.
Bulama Bukarti mai bincike kan Boko Haram ya ce shugaban ƙungiyar Muhammad Yusuf da jami'an tsaron Najeriya suka kashe ya taba bayar da labarin yadda ya tashi daga jihar Borno zuwa garin Mokwa a jihar Neja domin janyo ra'ayin Darul-salam ga shiga Boko Haram.
"Amma sun yi watsi da kiran shi na shiga Boko Haram, inda shi ma suka yi masa da'awa ya baro Maiduguri domin tana cike da ƙazanta suna so ya yi hijira ya dawo inda suke zaune."
"Daga karshe suka tashi, suka kafurta juna. suka kafurta Muhammad Yusuf, shi ma ya kafurta su," in ji Bukarti wanda ya ƙara da cewa ba sa ga-maciji domin an dade suna kafurta junansu.
A shekara ta 2009 ne, hukumomi a Najeriya suka tarwatsa 'yan kungiyar Darulsalam a garin Mokwa na jihar Neja, lamarin da ya kawo karshen wannan bangaren daga mazauninsu da aka sani.

Yanzu Darul-salam ta haɗa kai da Boko Haram ne?

Asalin hoton, Getty Images
Tun 2009 ake yaƙi da Boko Haram a Najeriya da kuma ƙasashen da ke kewaye da tafkin Chadi.
Boko Haram ana ganin ta warwatsu a sassan Najeriya da kuma ƙasashen Nijar da Kamaru. Kuma kamar yadda masana suka ce Darul-salam ta daɗe amma hare-haren da ake zargin sun kai wa wasu ƙauyuka a jihar Nasarawa ana ganin ko sun sauya tunani ko kuma sun ƙulla alaƙa da Boko Haram
Bukarti ya ce watsuwar Boko Haram arewa ta tsakiya a Najeriya, mai yiyuwa ne wasu daga cikin yan Boko Haram sun shiga Darul-salam.
Amma ya ce yanzu babu tabbas sai idan sojoji sun fitar da hujja kan makaman da suka ce sun kama da kuma kammala bincike kan waɗanda ke hannunsu a yanzu kafin gano yadda lamarin yake a yanzu.
"Wadannan mutanen 410 da sojoji suka ce sun kama, su kansu sojojin cewa suka yi su da kansu suka mika wuya. Ka ga kenen ba za ka ce sun turje wa sojoji ba."
Hatsarin Darul-salam ga tsaro
Masana na ganin Darul-salam na da hatsari sosai duk da cewa ba su riƙe da makamai, saboda yadda ba su yarda da gwamnati ba da hukunci da doka da oda da kuma jami'an tsaro ba.
"Kenan sun kafa ƙasa ne a cikin ƙasa. Ba su ɗauki shugaba Buhari ba a matsayin shugabansu haka ma gwamnan jihar Nasarawa," inji Bukarti.
Ya ce yanzu kamata ya yi hukumomin Najeriya su yi bincike domin idan mutanen nan ba su dauke da makamai, ba daidai ba ne a gurfanar da su a gaban kotu kan zarge-zargen ta'adanci.
"Kamata ya yi a kira su a zauna da su a mayar da su cikin gari su zauna cikin al'umma su kuma yadda da gwamnati da hukuncinta kamar yadda sauran yan Najeriya suka yarda."
Karin labarai da za ku so ku karanta:











