Kungiyar Darussalam: Sojojin Najeriya sun ce sun tarwatsa sansanin mayakan a jihar Nassarawa

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun tarwatsa wani sansanin masu tayar-da-kayar-baya da aka fi sani da Darussalam a yankin Uttu da kewaye da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa.
Rundunar ta ce dakarunta sun cimma sansanin `yan kungiyar ne tare da hadin gwiwar sauran jami`an tsaro, bayan sun tattara muhimman bayanai a kan maboyarsu.
Yayin harin rundunar ta ce jami'anta sun yi arangama da mayakan kungiyar wadanda daga bisani suka tsere, suka bar matansu, wadanda suka mika-wuya ga sojojin.
Kakakin cibiyar samar da bayanai a kan arangamar da sojojin Najeriya ke yi a sassan kasar Kwamanda Abdussalam Sani, ya shaida wa BBC cewa mutum fiye da dari hudu ne suka mika wuya, yawanci mata da kananan yara.
Ya ce, ''An samu wata cibiya da suke kera abubuwan fashewa, an kuma gano manyan bindigu guda shida, da buhun taki da suke amfani da shi da gurnet-gurnet''.
Ko kungiyar na da alaka da Boko Haram ?

Asalin hoton, Getty Images
Kwamanda Ibrahim Sani ya shaida wa BBC cewa, akwai alamun cewa suna da alaka da kungiyar Boko Haram, idan aka yi ;a'akari da yadda suke tafikar da ayyukansu.
`Yan kungiyar Darus- salam din dai, kamar yadda mazauna yankin Uttu ke cewa sun dade suna kai musu hari, har ta kai ga sun halaka mutane da dama,
Sun kuma kona garuruwan da ke kewaye, ciki har da garin Dausu, inda hakimin yankin yake, wanda shi da jama`arsu ala tilas suka koma zaman gdun-hijira a Umaisha.
Wannan tarwatsa maharan da aka yi ta sa mun fara sa-rai da komawa gida. inji Alhaji Idrisu Mundi Yakubu, hakimin Dausu:
A watan Mayun wannan shekarar ne gwamnatin jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana wanzuwar `yan kungiyar Darus-salam a jihar, wadanda ya ce sun addabi al`ummar karamar hukumar Toto da kewaye da hare-hare, kuma ba a dade ba sojojin Najeriyar suka ce dakarunsu sun gwabza da maharan, wadanda zuwa yanzu ba kai ga fayyace gangariyar manufarsu ba.










