Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hatsarin mota: An ayyana zaman makokin kwana uku a Zamfara na mutuwar mutum 17
Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ayyana zaman makoki na kwana uku sakamakon mutuwar wasu mutum 17.
Rundunar 'yan sanda jihar ta tabbatar da faruwar lamarin a kusa da garin Tsafe kan babban titin zuwa Sakkwato a ranar Laraba da yamma.
Cikin mutanen da hatsarin ya rutsa da su har da wasu da suka tarbi gwamnan jihar bayan komawarsa daga Abuja.
Wani mai taimaka wa gwamnan kan yaɗa labarai, Zailani Bappa ya shaida wa BBC cewa: ''A jiya Laraba bayan isowarmu da gwamnan, su waɗannan matasa sun tarbe mu a garin Tsafe, to wucewar mu ke da wuya muna wajen Kwatarkwashi sai muka sami labarin cewa sun yi hatsari bayan barin mu wajen.
''Daga nan sai gwamna ya ce mu juya. Sai muka samu wasu tireloli ne da dama mun ga wucewarsu irin masu tahowa daga Sakkwato ɗinnan, ashe ɗaya ta kufce ta murƙushe motocin matafiya har uku.''
Zailani ya ce hatsarin ya yi muni sosai don abun ba kyawun gani, wata motar ma an murtsuke ta cikin lambatu.
Ya ce tuni a lokacin aka fitar da gawarwakin aka kai kuma marasa lafiya asibiti.
''A yau da safe dai mun yi jana'izar mutum takwas, sannan sauran kuma danginsu sun yi jana'izarsu daban, sannan wasu mutum ukun har yanzu suna asibiti,'' in ji shi.
Sakamakon hakan ne gwamnan jihar Bello Matawalle ya ba da umarnin zaman makoki na kwana uku a jihar tare da sauke tutoci zuwa rabi.
Jami'in hulda da rundunar ƴan sandan jihar SP Muhammad Shehu ya ce lamarin da ya farun abu ne na alhini kuma tirelar ta taho ne daga jihar Sokoto.
Ya ce a yanzu haka an fara bincike don gano me ya jawo hatsarin domin a ɗauki matakin kare afkuwar irinsa a nan gaba.
Me ganau suka ce?
Wani da ya shaida lamarin mai suna Bilyaminu wanda motar da yake ciki take kan titi lokacin da abin ya faru, ya shaida wa BBC cewa wani mai ƙaramar mota ƙirar Golf ne ya taho da gudu yana ƙoƙarin yin oba tekin, sai ya gaza yi don hannunsa ya yi nauyi, a haka sai ya bugarwa mai tirela taya.
''Sai motarsa ta birkice shi kuma mai tirelar ashe tayar da aka bugar masa ta kauce, to a ƙoƙarinsa na shawo kan abin sai ya kauce ya je ya bugi wata ƙaramar motar da ta sauka daga hanya sai ya haye kanta.
''Akwai kuma wata Golf ɗin da ta ƙara zuwa ta bugi tirelar ita ma ta kife. Ni dai a gabana mun kwashi mutum tara a lokacin.
''Amma wasu mutum taran da tirelar ta danne sai da aka kwashe siminti sannan aka samu aka ciro su.
Bilyamnu ya ce bai taɓa ganin wani bala'i a rayuwarsa irin na wanda ya gani jiya a wajen hatsarin ba.
''Wallahi ruwa ake amma na manta ruwan ake yi, duk da dukanmu da yake yi. Wani lokacin za a yi hatsari ka ga mutane suna satar abubuwa amma jiya kam kowa a ruɗe yake yana ƙoƙarin taimaka wa a ceto ƴan uwa.
''Gwamna ma bai san abin da ya faru ba don ya riga ya wuce. Amma ana gaya masa sai ga shi ya juyo a gabansa aka kwashe mutanen nan sannan ya wuce,'' in ji Bilyaminu.
Motocin da suka yi hatsarin duk ƙirar Golf ne amma yawancinsu duk sun malkwaɗe tare da kwankwatsewa.