Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG vs Bayern: Tarihi za a kafa ko maimaita kansa zai yi?
Shakka babu wasa kowanne iri ne tsakanin Paris Saint-Germain da Bayern Munich zai yi zafi sosai, ballantana kuma a ce wasan ƙarshe na gasar Champions League - wanda da ma gasar zakaru ce.
Sai dai abin tambayar shi ne: Shin PSG ce za ta kafa tarihi ko kuma Baryern ce za ta ɗaga kofin a karo na shida?
Wannan ne karon farko da PSG take zuwa wasan ƙarshe a gasar ta Champions League kuma wannan zubin 'yan wasan na mai horaswa Thomas Tuchel, su ne na 41 da suka samu halartar gasar a tarihin ƙungiyar.
Wasan wanda za a take da ƙarfe 8:00 na dare agogon Najeriya da Nijar, za a buga shi ne a birnin Lisbon na ƙasar Portugal kamar yadda aka buga sauran wasanni tun daga matakin 'yan 16 - za ku iya biyo mu a wannan shafin domin ganin yadda za ta kasance.
Suna cikin ƙungiyoyin da suka fi kowa kashe kuɗi a Nahiyar Turai sannan kuma suna cikin waɗanda suka fi kowa rashin taɓuka abin kirki.
Tuchel ya haɗa ƙungiya mai hazaƙa a wannan karo kuma ya samar wa tauraron ɗan wasa Neymar wani dandali da yake taka leda mafi ƙayatarwa cikin shekara uku da ya shafe a kulob ɗin.
Babu mamaki a wannan karo Neymar ya cimma abin da ya kawo shi ƙungiyar, ganin yadda ya ci ƙwallo 16 da bayarwa a ci 20 a dukkanin gasa a kakar bana.
Bayan lashe Bundesliga da tazarar maki 13 da kuma German Cup, tawagar mai horarwa Hansi Flick na kan hanyarta ta maimaita abin da tawagar ƙungiyar ta shekarar 2012-2013 ta yi.
"Tawagar Bayern ta 2013 ta fi ta yanzu ƙwarewa matuƙa amma kuma akwai 'yan wasan da ba lallai su samu shiga wannan tawagar ta bana ba," a cewar masanin ƙwallon gasar Bundesliga, Raphael Honigstein.
Bayern ta ci dukkanin wasanta a wannan gasa ta bana, ciki har da 8-2 da suka yi wa Barcelona mahangurɓa a wasan kwata fayinal.
Robert Lewandowski ya ci ƙwallo a wasa tara a jere a Champions League, wanda Cristiano Ronaldo kawai ya fi shi zira ƙwallaye a wasanni a jere. Sannan kuma ga Serge Gnabry wanda ya ci ƙallo biyu a wasansu da Barcelona.
"Lewandowski ba ya nuna azama wurin cin ƙwallo a kwanan nan kamar Gnabry amma har yanzu yana cin kwallaye. Kuma suna da 'yan wasan gefe mafiya kwarewa a duniya," in ji Honigstein.
Idan PSG ta lashe wannan gasa, shakka babu za a fara daukarta a matsayin babba a Turai idan aka kwatanta da irin kashin da Barcelona ta ba ta na 6-1 a 2017.