Premier League: Za a fara wasan gasar da fafatawar zakaru

An wallafa

Zakarun gasar Premier Liverpool za su kara da zakarun gasar Championship Leeds United a wasan farko na bude kakar 2020-21.

Fulham da ta samu tsallakawa Premier bayan wasan samun gurbi za ta kara da Arsenal yayin da West Bromwich Albion za ta kara da Leicester United da ta kare Premier a ta uku.

Wasan farkon da za a buga za a yi shi ne ranar 12 ga watan Satumba.

Kazalika za a duba lokacin da Manchester City da Aston Villa za su yi wasansu, haka ma Burnely da Manchester United saboda wasannin gasar Turai da suka buga a baya-bayan nan.

Chelsea da Wolverhampton Wanderers za su buga nasu wasan a ranar Litinin 14 ga watan Satumba suma saboda fitar da su da aka yi daga gasar Europa.

Chelsea za ta kara da Brighton yayin da Wolves za ta je Sheffield United.

Sauran wasannin da za a buga a karshen makon Crystal Palace da Southampton sai Tottenham da Everton da kuma West Ham United da Newcastle United.

Za a sanar da lokacin da za a fara wasa bayan zaben gidan latabijin din da zai dauki nauyin nuna gasar, kuma za a buga wasannin ne ba tare da 'yan kallo saboda wannan annoba ta korona.

Jadawalin gasar Premeir Ingila (za a sanar da lokacin da za a fara wasannin)

Crystal Palace da Southampton (12 Satumba)

Fulham da Arsenal (12 Satumba))

Liverpool da Leeds United (12 Satumba))

Tottenham Hotspur da Everton (12 Satumba))

West Bromwich Albion da Leicester City (12 Satumba))

West Ham United da Newcastle United (12 Satumba))

Brighton da Chelsea (14 Satumba))

Sheffield United da Wolves (14 Satumba)

Burnley da Manchester United (za a buga daga baya)

Manchester City da Aston Villa (za a buga daga baya)

Zababbun wasannin hamayya da ranarakunsu...

  • 17 Oktoba - Everton da Liverpool
  • 5 Disamba - Tottenham Hotspur da Arsenal
  • 12 Disamba - Manchester United da Manchester City
  • 16 Janairu - Wolves da West Brom
  • 20 Fabirairu - Liverpool da Everton
  • 6 Maris - Manchester City da Manchester United
  • 13 Maris - Arsenal da Tottenham Hotspur
  • 1 Mayu - West Brom da Wolves