Hotunan Afirka na wannan makon: daga 7 zuwa 13 ga watan Agusta 2020

An wallafa

Zababbun hotunan Afirka da 'yan Afirka a wata nahiyar na wannan makon:

Starlings are seen in the Amboseli National Park, Kenya. Their feathers are a combination of bright blue, purple, black, white and brown.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu tsuntsaye a gidan kiwon namun daji na Amboseli da ke kasar Kenya ranar Laraba.
Children stand in social distancing squares on arrival at school.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yara 'yan makaranta sanye da takunkumi suna jira a kan layi a wata makaranta da ke Johannesburg, babban birnin Afirka ta Kudu ranar Alhamis.
People look at the carcass of a Brydes Whale on Kommetjie beach in Cape Town.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Litinin, wadannan mutanen da suka je bakin teku sun ga gawar dabbar ruwa mai suna whale wacce ruwa ya turo gabar teku a birnin Cape Town.
A meteor streaks past stars in the night sky during the annual Perseid meteor shower.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Laraba a sararin samaniyar da ke iyakar Masar da Isra'ila, an hango wasu nau'uka na taurari suna shawagi.
People stand at the entrance to a school used as a polling station. One wall is daubed with a large, smiley face.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tun da farko a ranar ta Laraba, masu zabe a birnin Alkahira da sauran sassan Masar sun kada kuri'unsu a zaben 'yan majalisar dattawa.
A woman enters a row of kiosks that are flooded.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Lahadi, wannan mai shagon da ke Bor, Sudan ta Kudu, yana duba irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi masa. Lamarin ya faru ne sanadin mamakon ruwan sama da kuma Kogin Nilu ya cika sosai, inda ya tilasta wa mutane tserewa daga gidajensu.
Worshippers sit inside and pray.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Musulmi sun halarci sallar Juma'a karon farko cikin wata hudu a birnin Lagos da ke Najeriya.
Kenyan workers protest outside their consulate in Beirut, Lebanon.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, "Muna son tafiya gida," in ji ma'aikatan kasar Kenya lokacin gangamin da suka yi a wajen ofishin jakadancin Beirut ranar Litinin. Ma'aikata bakin haure suna korafi kan zargin cin zarafinsu. Kwana kadan kafin nan, wasu abubuwa sun fashe a babban birnin na Lebanon lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 100, sannan dubbai suka jikkata.
A drone image shows the oil spillage near the area where the bulk carrier ship MV Wakashio, belonging to a Japanese company but Panamanian-flagged, ran aground on a reef, at Riviere des Creoles, Mauritius.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Talata, man fetur ya tsiyaye bayan wani jirgin ruwa ya ci kasa a Mauritius...
A volunteer stands in the sludge which he handles with gloved hands.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Dubban masu aikin sa-kai sun yi aikin kwashe dagwalo, wanda masana suka ce zai yi lalata halittun ruwa.

Hotuna daga Reuters, AFP da EPA.