Fyaɗe: 'Idan ana kashe masu cin zarafin yara ta hanyar lalata za a samu raguwar matsalar'

An wallafa

Wasu daga cikin iyayen da aka yi wa 'ya'yansu fyaɗe a jihar Kano daga arewa maso yammacin Najeriya sun nuna goyan bayansu kan hukuncin da wata babbar kotun Musulunci ta yi na yanke wa wani tsoho hukuncin kisa kan laifin fyaɗe.

Iyayen na da ra'ayin cewar hukuncin zai yi tasiri wajen magance yawaitar aikata laifin, amma sai sun ce akwai bukatar gwamnati ta gaggauta tabbatar da hukuncin da kotu ta yanke ga masu laifin.

Wani mahaifi da aka yi wa 'yarsa mai shekara 12 fyaɗe shekaru biyu da suka gabata, da har yanzu suke kotu, ya shaida wa BBC cewa wannan hukunci ya yi masa daɗi, duk kuwa da ba wanda ya yi wa 'yar tasa fyaɗen aka hukunta ba.

"Irin hakan ya dace a matsayinmu na Musulmai da kuma yadda rayuwar al'umma ke tafiya. Idan har aka ce a rayuwar nan za a dinga abubuwa irin fyaɗe to ɗan adam zai zama ba shi da wata daraja."

"Na farko idan ka duba za ka ga cewa tarihin yaron da aka yi wa hakan zai taɓu, kuma hkan na iya jefa rayuwar yaran cikin wani yanayi da ka iya ɓata musu halayya ma,' kamar yadda mutumin wanda muka ɓoye sunansa ya shaida wa wakilinmu na Kano Khalifa Shehu Dokaji.

A ganinsa irin wannan hukunci da aka ɗauka na kisan wanda aka kama da laifin fyaɗe zai taimaka wajen rage yawaitar laifin, ''musamman idan aka ce an kashe mutum 100 da aka samu da laifin to suran za su shiga taitayinsu in ji shi.''

Mahaifin ya kara da cewa: ''Ina kira ga gwamnati don Allah don Annabi ta sa ido ta kuma sa mutanen da za su zama sahihai a kan irin waɗannan al'amura, a dinga bibiyar lamuran idan suka faru, a kuma yi saurin yanke hukunci idan har an same su da wannan laifi.

'Ni ma batun 'yata na kotu'

Mutumin ya shaida wa BBC cewa shekara biyu da suka gabata shi ma an yi wa 'yarsa mai shekara 12 fyaɗe, kuma har yanzu batun na kotu ba a kammala shari'ar ba.

''Yanzu dai muna jiran zama na gaba a kotu don jin yadda shari'ar za ta kaya.''

Ya ce a lokacin da aka yi mata fyaɗen al'amura sun dagule musu don har sai da 'yar tasa ta daina zuwa makaranta saboda tsangwamarta da ake yi a makaranta da cikin unguwa.

''Har ta kai ta kawo idan ta fita sai yara su dinga bin ta suna mata sowa ye ga wance da aka yi wa kaza da kaza, ba ma jin daɗin hakan ko kaɗan. An lalata rayuwar 'yarmu, mu kanmu ba mu da kwanciyar hankali muna cikin damuwa sosai.

Uban ya ce lokacin da abin ya faru yarinyar ba ta iya riƙe fitsari har sai da ta kai ana sa mata ƙunzugu. ''Yanzu Alhamdulillah amma har yanzu ba ta iya riƙe fitsarina tsawon lokaci. Kuma tuni ta koma makaranta.

Karin labaran da ke da alaƙa da wannan