Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid: Bale ɓata lokaci kawai yake yi a Bernabeu – Calderon
Gareth Bale na "ɓata lokaci ne" kawai a Bernabeu kuma wajibi ne ƙungiyar da ɗan wasan su kawo ƙarshen wannan matsalar nan da ƙarshen nan 'yan watanni, in ji tsohon shugaban Real Madrid Ramon Calderon.
Ɗan wasan gaban na Wales mai shekara 31 bai buga wasan da Manchester City ta doke Madrid ba a Champions League ranar Juama'a, yayin da koci Zinedine Zidane ke cewa "shi ya ga damar ƙin buga wasan".
"Abin baƙin ciki ne. Abin tausayi ne a riƙa ganin ɗan wasa kamarsa ba a cikin fili ba," a cewar Calderon game da halin da ɗan wasan yake ciki a yanzu.
"Ina ganin har yanzu ƙwarewarsa tana nan, har yanzu haziƙin ɗan wasa ne da zai iya ci gaba da taka leda a babbar ƙungiya a faɗin duniya.
"Saboda haka ya zama dole su nemi hanyar sasantawa domin muradinsu duka.
"Idan ba zai rage albashinsa ba, ba matsala, dole ne dai su nemi hanyar magance matsalar."
Shekara biyu ta rage a yarjejeniyar da Bale ya ƙulla da Madrid, wadda ake biyansa kusan fan 600,000 duk mako.
Wasa 14 kacal aka fara da shi a dukkanin gasar da Madrid ta buga a bana kuma wasa biyu kacal ya buga tun bayan dawowa daga hutun annobar korona a watan Yuni.