Hotunan Afirka na wannan makon daga 31 ga watan Yuli zuwa - 6 ga watan Agusta 2020

An wallafa

Mun zabo muku wasu daga cikin kayatattun hotunan Afirka na wannan makon:

Kenyan fashionista James Maina Mwangi, dressed all in purple, stands beside green, yellow and red suits.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Fittacen dan gayu na Kenya James Maina Mwangi, wanda ya cewa BBC duk Afrika babu wanda ya kai shi gayu, ya tsaya a gefen jerin tufafinsa ranar Juma'a.
Girls wearing new clothes are pictured on the first day of Eid al-Adha in Dakar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar ce kuma a Dakar babban birnin Senegal, wadannan yaran sanye tufafi masu kyawu suka yi bikin babbar Sallah...
A boy tries to inflate a balloon.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Haka kuma a Dakar an dauki hoton wannan yaron yana wasa da balan-balan.
People touch a depiction of the Virgin Mary after a mass at Cairo's Historical Church of Blessed Virgin Mary.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kristoci Kifdawa sun dafa hoton da aka ce na Maryam mahaifiyar annabi Isa ce bayan an sake bude cocin kasar Masar ranar Litinin.
A bronze-coloured statue is fitted with a mask with a caption that reads "stay safe".

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Litinin, an ga wasu mutum mutumi sanye da takunkumin rufe fuska a birnin Lagos domin tunatarwa ga jama'a
Tunisian singer and violinist Yasmine Azaiez performs on stage.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Laraba, mawakiyar kasar Tunisia Yasmine Azaiez, tana waka a wajen bikin Hammamet na duniya.
Naval officers await the arrival of President Patrice Talon at the Palais de la Marina.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mambobin rundunar sojan ruwan Benin, a tsaye a wajen fadar shugaban kasa da ke Cotonou ranar Asabar gabanin bikin zagayowar ranar samun 'yanci.
Men stand by boats as the sun is low in the sky in Al Maadea district of Behera Governorate.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masunta a arewancin Masar suna shirin shiga kwale-kwalenu don tafiya kamun kifi ranar Talata.

An samo dukkan hotunan ne daga Reuters da AFP da EPA.