Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Uganda: Shugaba Museveni ya saki bidiyo yana atisaye a gida
Shugaban Uganda Yoweri Museveni, ya sake wallafa wani bidiyo a karo na biyu yana yin atisaye a gidansa, da manufar ba da ƙwarin gwiwa ga mutane su riƙa atisaye a gida yayin annobar korona.
An nuno shugaban mai shekara 75 yana sassarfa a wani ɗaki, kafin daga bisani ya zo ya yi wani atisaye na kirji da hannu sau 40 wata 'yar karamar murya na kirga masa.
Ya ce wannan wani kalubale ne ga (bazukulu) yadda ake kiran samarin ƙasar kenan cikin wasa, wanda kuma tuni wasu suka soma yin abin da ya kalubalance su a kai.
Ga dai bidiyon:
Shugaba Museveni, ya saki irin wannan bidiyon a watan Afrilu bayan dakatar da atisaye a bainar jama'a a wani mataki na shawo kan annobar korona. Amma daga baya an janye matakin.
Za a gudanar da zaɓen ƙasar a watan Janairun 2021, amma hukumar zaɓe ta ƙasar ta haramta gangamin zabe, tana shawartar 'yan takarar da su yi gangamin ta talabijin da radiyo.