Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kantin Shoprite na duba yiwuwar janye harkokin kasuwancinsa daga Najeriya
Babban kantin nan na sayar da kayayyaki Shoprite ya ce yana duba yiwuwar daina gudanar da harkokin kasuwancinsa a Najeriya.
Wata sanarwa da ya fitar ranar litinin da safe ta ce masu kantin sun dauki matakin janyewa daga Najeriya ne saboda an samu mutanen da suka nuna sha'awar sayensa.
Shoprite ya bayyana Najeriya a rukunin kasashen da "za a daina gudanar da harkoki" a yayin da ya sanar da raguwar kashi 5.9 cikin dari na kasuwarsa a kasar a 2019 da kuma kashi 6.4 daga watan Janairu zuwa Yuni na 2020 saboda annobar korona.
Babban kantin ya ce annobar korona ta yi tasiri sosai a kan harkokin kasuwancinsa na kasashe 14 a Afirka inda aka samu raguwar sayen kayansa da kashi 1.4, ko da yake a Afirka ta Kudi an samu "gagatrumar karuwa ta kasuwancinmu".
Mai magana da yawun babban kantin a Najeriya, Mr. Ini Achibong, ya shaida wa BBC masu kantin sun dade suna neman mutanen da za su saye shi kouma babu abin da zai sauya game da yadda yake gudanar da harkokinsa a kasar a wannan lokaci.
Shoprite ya bude kanti a Najeriya ne a 2005, wanda ya bayyana a matsayin inda yake "sayar da dukkan, ko akasarin kayansa."
A shekarar da ta wuce, matasa sun kai harin ramuwar gayya kan wasu kantunan na Shoprite da ke Najeriya sakamakon zargin musnugawa wasu 'yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu.
Matasa da dama kan yi wa kantin Shoprite tsinke a lokutan bukukuwa inda suke yin sayayya sannan su dauki hotuna.
Ra'ayoyin Najeriya kan wannan batun: