Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsaloli biyu da ke addabar Gwamna Badaru na Jigawa
Gwamna Badaru Abubakar na Jihar Jigawa ya ce rashin dogaro da kai wurin kuɗaɗen shiga na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ci masa tuwo a ƙwarya a mulkin jihar.
Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana hakan ne a cikin shirin A Faɗa A Cika na BBC Hausa wanda ke da haɗin gwiwa da Gidauniyar MacArthur.
Badaru Abubakar shi ne gwamnan jihar Jigawa na uku bayan komawar Najeriya bisa tafarkin mulkin demokradiyya a shekara ta 1999.
Ya ce akwai wasu matsaloli guda biyu da suka fi ci masa tuwo a kwarya a harkar tafiyar da mulkin jihar: rashin dogaro da kai wurin kuɗaɗen shiga da kuma tabarbarewar ilimi.
An tambayi gwamnan, 'shin mene ne ya fi ci maka tuwo a ƙwarya cikin shekara biyar da ka kwashe kana mulkin jihar Jigawa?'
Sai ya ce: "Idan na duba tattalin arzikin duniya, da yadda Najeriya ta dogara da mai, da kuma yadda mu a Jigawa muka dogara kusan kashi casa'in bisa ɗari a kan kuɗaɗen da ake aika wa daga gwamnatin tarayya, wato grant. Me zai faru da Jihar Jigawa idan wannan kuɗin ya samu tsaiko ba ya zuwa?
Ya ƙara da cewa: "Na biyun su shi ne maganar gyaran harkar ilimi ba ƙaramin aiki ba ne wanda yake sai an haɗa da addu'a da jajircewa, sai kowa ya sa hannu za a gyara shi kamar yadda muke so."
A cewar sa, wannan ne ya sa gwamnatinsa ta mayar da hankali wurin samar wa mutane aikin yi da kuma ƙarfafa tattalin arziƙin jihar Jigawa ta hanyar samar da masana'antu yadda harajin da gwamnati ke karɓa zai iya rike ta.
A lokacin tattaunawar ta sa'a ɗaya, gwamnan ya amsa tambayoyi da dama a kan irin alƙawuran da ya ɗauka gabanin hawan sa mulki da kuma bayan hawan sa kan karaga.